Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Thursday, April 19, 2018

Rikicin manoma da makiyaya ya hana yara dubu 300 zuwa makaranta a Najeriya



Yara kanana kimanin dubu 300 ne ba sa zuwa makaranta a tsakiyar Najeriya sakamakon yawan rikicin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya.
Sakatare Janar na Hukumar bayar da Ilimi ta jihar benue Farfesa Wilfred Uji ya ce, rikicin da ake ci gaba da yi a jihar na shafar ilimin yara kanana.
Uji ya ce “A fadin jihar akwai ‘yan makarantar babbar sakandire dubu 200 da na karamar sakandire dubu 100 da ba sa zuwa makaranta.”
Farfesa Uji ya kara da cewa, rikicin na yi wa malamai barazana a jihar.

No comments:

Post a Comment