Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Thursday, April 19, 2018

Mutumin da yafi kowa tsufa a duniya ya rasu


An bayyana rasuwar Celino Villanueva Jaramillo mai shekaru 121 dan kasar Chile da ake kirarin yafi kowa tsufa a duniya.
Jaramillo, ya rasu ne a lokacin da yake jinya a asibitin Chile dake garin  San José de Mariquina.
Jaramillo da aka haifa a ranar 25 ga watan Yulin 1896 sanadiyar rashin samun takardar shaidar haihuwarsa bai samu shiga cikin littafin kundin tarihin duniya mai suna 'Guinnes Bokk of Record' ba, amma duk da haka an bayyana shi a matsayin wanda yafi kowa yawan shekaru a duniya.
Jaramillo wanda ya fado daga kan gado, lamarin da yayi sanadiyar kariyar awazunsa uku tare da sukar hantarsa, baida dangi ko daya da suka saura a duniya.
Celino Villanueva Jaramillo, wanda ya kasance manomi, za'a yi zana'izarsa a gobe juma'a a garin San José de Mariquina daga bisani kuma a binne shi a makabartar garin Mehuín .

No comments:

Post a Comment