Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Wednesday, April 18, 2018

Cutar zazzabin Lassa na kara yadu wa a Najeriya



Jami’an Ma’aikatar Yada Labarai ta Najeriya Abubakar Muhammad ya fitar da sanarwa ga manema labarai cewa, mutum 1 ya mutu inda wasu ke kwance a asibiti sakamakon kamu wa da cutar zazzabin lassa a garin Yolan jihar Adamawa ta Kasar.
Muhammad ya ce, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayyar tare da Hadin Gwiwar Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO sun samar da asibitin musamman don shawo kan cutar a jihar Adamawa.
Sanarwar da Hukumar Yaki da Cututtuka ta Najeriya ta fitar ta ce, daga watan Janairu zuwa yau mutane 110 cutar ta kashe kuma a jihohi 18 mutane dubu 3,126 ne suka kamu da cutar.
Ana kamu wa da cutar Lassadaga kashin bera wadda mutum na iya harba wa wani mutumin.
Gwamnati ta gargadi jama’a da su kasance cikin tsafta a koyaushe.

No comments:

Post a Comment