Dr. Saleh Kaura :
WACE CE UWAR DAN DA AKA HAIFA TA WADANNAN HANYOYI?
Game mas’alar wace ce uwa ta hakika ga jariri da aka haifa ta daya daga cikin wadannan hanyoyi, shin uwar ita ce mai mahaifa, ko kuwa ita ce wadda aka ciro kwayoyin halitta daga maniyyinta?
A nan malamai sun sami sabani, wasu sun tafi akan cewa: mai mahaifa ce uwa ta hakika, sa’ilin da wasu kuma suka tafi akan cewa: mai kwayoyin halitta ce uwa ga jaririn da aka haifa, bari mu kawo dalilan da kowane bangare ya dogara da su, sannan mu ambaci fatawar da ta fi karfin dalilai.
1 - Masu cewa: Uwa ita ce mai mahaifa:
A wurin wannan sashe na malamai, ana danganta dan da aka haifa ta hanyar “Hayar Mahaifa” ko ta hanyar “sayar, ko kyautar da kwayoyin halitta” da uwar da ta dauki cikinsa a cikin mahaifarta ne, ba a danganta shi da mace mai kwayoyin halittar, duk wani hakki, ko hukunci na uwa da kusanci za su tabbata wa mai mahaifa ce, dalilan da aka dogara da su a nan sun hada:
Dalili na farko: Akwai ayoyin Alkur’ani Mai girma da dama da suka tabbatar da cewa uwa ita ce wadda ta dauki ciki har zuwa haihuwa, saboda haka wadda aka sanya maniyyi da kwayoyin halittar a cikin mahaifarta ita ce uwa, Allah Madaukacin Sarki ya fadi a cikin suratun Nahl cewa: ((Allah ne ya fitar da ku daga cikin cikin iyayenku mata a lokacin ba ku san komai ba….)) [an-Nahl: 78], a wannan ayar Allah Madaukakin Sarki ya bayyana cewa wadda jariri ya fito daga cikinta ita ce: uwa, shi kuwa jariri yana fitowa ne daga mahaifar wadda ta dauki ciki.
Sannan a suratu Lukman Allah Mai girma da daukaka ya ce: ((Mun yi wa mutum wasici da mahaifansa kan ya kyautata masu kwarai da gaske, mahaifiyarsa ce ta dauki cikinsa cikin wahalhalu masu bin juna…)) [Lukman: 14], a nan ma Allah Madaukakin Sarki ya bayyana cewa: uwa ta hakika ita ce wadda ta dauki cikin jariri a mahaifarta..
A kuma suratul Ahkaf, Allah Madaukakin Sarki ya ce: ((Mun yi wa mutum wasici da mahaifansa kan ya kyautata masu kwarai da gaske, mahaifiyarsa ce ta dauki cikinsa cikin wahala, ta kuma haife shi cikin wahala…)) [al-Ahkaf: 15], a nan kuma ayar ta bayyana cewa wadda ta sha wahalhalun ciki ita ce uwa ta hakika.
Koda dai an bayar da amsa game da kafa hujja da wadannan ayoyin da cewa: ai ma’anar uwa a lokacin saukar wadannan ayoyin ta saba da ma’anar uwar a cikin wannan mas’ala da ake magana akanta a yanzu; domin uwa a wancan lokacin ita ce: mai mahaifa gami da kwayoyin halitta a hade duk a lokaci daya, ma’ana kowane jariri yana da hanyoyi biyu da yake da dangantaka da uwarsa: Na farko: kwayoyin halittar da yake gadon wasu sifofi na musamman daga gareta. Na biyu kuma: mahaifar da yake samu ya fake har zuwa ya gama zamowa cikakken mutumin da zai iya fara gwagwarmayar rayuwa. Saboda haka, kiran wadda ta dauki ciki da wahalhalunci ciki da haihuwa da cewa ita ce uwa ta hakika, ba tare da ita ce mai kwayoyin halitta ba, abu ne da ya saba da ma’anar uwar da wadannan ayoyi suka bayyana a lokacin da aka saukar da su.
Dalili na biyu: Haka ma Alkur’ani Mai girma ya bayyana sifar uwar da ita ce ta dauki ciki a mahaifarta, ta kuma haife da wani salo da yake nuna cewa jaririn da ta haifa nata ne, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: ((.. Kada a cutar da mahaifiya ta hanyar danta..)) [al-Bakra:233], kuma mahaifiya ta ainihi ita ce wadda ta durkusa ta haifa.
A wata ayar a suratul Mujadala kuma, Allah Mai girma da daukaka yana fadi cewa: ((Lallai wadanda suke sifanta mãtãnsu –daga cikinku- da mahaifansu mãtã wajen haramci sun yi kuskure; domin mãtãn nasu ba su ne iyayensu ba, iyayensu mãtã na gaskiya ba wasu ba ne ban da wadanda suka haife su..)) [al-Mujadalah: 2], a nan ma Allah Mai girma ya bayyana a fili cewa uwa ita ce wadda ta durkusa ta haifa..
Dalili na uku: Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana fadi a Hadisin da Sayyiduna Abdullahi Bn Mas’ud (Allah ya kara yarda da shi) ya ruwaito, cewa: ((Lallai ana hada halittar kowane dayanku a cikin mahaifiyarsa, kwanaki arba'in yana maniyyi, sannan ya zama gudan jini gwargwadon haka, sannan ya zama tsokan nama na kwanaki arba'in..)) [al-Bukhari da Muslim], Anan ma Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya kira wadda aka hada halittar jariri a cikin mahaifarta da sunan uwa.
Wannan hukunci zai haifar da tambaya mai kama da haka: Idan uwa ta hakika ita ce wadda ta dauki ciki har zuwa haihuwa, -kaman yanda malamai masu wannan fahimta suka tafi a kai-, to mene ne dangantakar wannan jaririn da matar da aka yi amfani da kwayoyin halittar da aka ciro daga maniyyinta?..
Amsa a nan ita ce: Su kansu wadannan malamai suna da fahimta iri biyu ne a wannan mas’alar:
FAHIMTA TA FARKO: Wadda kungiyar “alMajma’ul Fikhil Islamiy” ta tafi a kai a taronta mai lamba bakwai da aka yi a Makka a shekara 1404 bayan hijira, daidai da 1984 Miladiyya, suna ganin cewa: duk da dai ita mai kwayoyin halittar ba ita ce uwarsa a Shari’ance ba, sai dai kuma ba za ta rasa dangantaka da shi ba, saboda haka suka ce: daidai take da uwar da ta shayar da shi; dalilinsu kuwa shi ne: dalilin da ya sanya wadda ta shayar da jariri ta zamo muharramar jariri shi ne gudummuwar da ta bayar wajen samar, ko habakar wani sashe na jikin jaririn, ku kuma alal akalla akwai shubuhar haka, saboda haka mafi karancin abin da za a fadi a nan shi ne: wannan jariri yana da wani sashe na wannan mata mai kwayoyin halitta, sai ta zamo muharramarsa, kaman yanda wadda ta shayar da shi take zamowa muharrama a gare shi.
FAHIMTA BIYU: Masu wannan fahimtar kuma sun tafi akan cewa babu wata dangataka tsakanin jaririn da mace mai kwayoyin halittar kwata-kwata, saboda haka, abin da ta yi na bayar da kwayoyin halitta ba shi da wani tasiri.. dalilinsu kuwa shi ne: abubuwa uku ne suka haramta aure har abada da mace: dangi daya, surukuta, da kuma shayarwa. Dan da hukunce-hukuncen Shari’a suke hawa kansa shi ne dan da Shari’a ta yarda da shi, a nan kuma abin ba haka ba ne.
2 - Masu cewa: Uwa ita ce mai kwayoyin halitta:
Wasu daga cikin malamai kuma sun tafi akan cewa uwar dan da aka samu ta wadannan hanyoyin ta ainihi ita ce: mai kwayoyin halitta, wannan fahimta –a asali- ta masu ganin cewa ya halatta a bayar da hayar mahaifa ne a duka surorin da muka bayyana (Malamai ba su lura da masu wannan fahimtar, saboda bayyanar raunin hujjojin da suka dogara da su; domin ba kowane sabani ne ake lura da shi ba), sannan kuma masu fahimtar halaccin idan mahaifar ta kishiya ce suka mara masu baya.
Bari yanzu mu kawo hujjojin nasu, sannan mu fadi amsoshin da aka ba su a takaice:
Hujja ta farko: Sun ce: Allah Madaukakin Sarki ya nuna muhimmancin kwayoyin halitta wajen tabbatar da dangataka, bal ma, akwai wurare masu yawa da ya tabbatar da cewa digon maniyyi shi ne asalin dan Adam, ga wasu daga cikin ayoyin da suke tabbatar da haka:
1 - Allah Madaukakin Sarki yana cewa: ((Ya halicce mutum daga digon maniyyi; sai kuma gas hi ya zamo mai yawan bayyanar da husuma)) [an-Nahl:4].
2 - A wani wurin kuma Madaukakin Sarki yana cewa: ((Lallai mu ne muka halicce ku daga turbaya, sannan daga digon maniyyi, sannan daga gudan jini, sannan tsokar da take dauke da surar dan Adam da ma wadda ba ta dauke da surarsa……….)) [al-Hajji: 5].
3 - Mai girma da daukaka ya kuma sake cewa: ((Shi ne wanda ya halicce ku daga turbaya, sannan daga digon maniyyi, sannan daga gudan jini..)) [Ghafir: 67].
4 - A wani wurin kuma ya ce: ((Kuma lallai shi ne ya halicci abubuwa biyu-biyu, na miji da mace cikin mutane da dabbobi… daga maniyyi mai tunkudowa)) [an-Najm: 45-46].
5 - Haka ma Allah Buwayi gagara misali yana cewa: ((Shin shi wannan dan Adam bai kasance digon maniyyi da aka kaddara tsara shi a cikin mahaifa ba?)) [al-Kiyama: 37].
Wadannan ayoyin sun nuna cewa an halicci dan Adam ne daga digon maniyyi, sannan daga baya ya bi wasu matakai har zuwa lokacin da aka haife shi, hakan yana nuna cewa ana danganta da ne zuwa ga mai kwayoyin halitta, wadda kuma a nan ita cewa wadda aka hada maniyyin mijinta da kwayoyin halittar da aka ciro daga maniyyinta..
AMSA: An mayar wa masu wannan ra’ayin amsa da cewa: a nan fa wadannan ayoyi suna magana ne idan ruwan maniyyin namijin da kwayoyin halittar mace sun kiyaye hukuncin Shari’a a lokacin fitowarsu, da kuma lokacin shigar da su cikin mahaifa kenan, idan ba a kiyaye hukuncin Shari’a ba, to ba su da wata kima da daraja; saboda haka, kwayoyin halittar da suke da kima da daraja a mahangar Shari’ar Musulunci su ne wadanda suka mutunta tsarin Shari’a, kuma da su ne ake tabbatar da tsatso da dangane, dole ne su zamo sun hadu ne a sanadiyyar aure da shaidu, ita kuwa mai mahaifar haya, ko na aro ba matar mai maniyyin ba ce, babu kuma wani dalili da yake nuna cewa ita matarsa ce. Duk da cewa kowa ya sani cewa: mazinace shi ne mai da idan ya yi zina har aka sami ciki a likitance, amma ita Shari’a babu ruwanta da wannan dalili, domin ba uba ne shi ba a Shari’ance.
Hujja ta biyu: Dan da aka haifa ta wadannan hanyoyi bai amfana da matar mai mahaifa da komai da ya wuce abincin da zai sanya ya girma, kana ya habaka har zuwa lokacin da za a haife shi, saboda haka za a iya kamanta shi da jaririn da yake samun abincinsa ba daga mahaifiyarsa ba.
AMSA: Lallai ilimi ya tabbatar da cewa mahaifa tana da tasiri wajen samar da sifofin halitta ga jariri, ba wai kawai taimakawa take yi ba, ita da kanta akwai sifofin da daga ita ake samu.
Hujja ta uku: Sun kafa hujja ta hanyar kiyasi da amfanin gona, inda suka ce: amfanin gona da ake samu yana zuwa ne da irin da aka shuka, ba daga kasar da aka binne ba, idan ka shuka irin shinkafa a kowace irin kasa, to shinkafa ce za ta fito, haka ma idan ka shuka irin lemo a kowace kasa, to lemo ne za a girba. Saboda haka, duk da cewa kasa ita ce take taimaka wa irin da aka shuka na ya girma, ya kuma bunkasa, sai dai ba ta da ta-cewa wajen nau’i, ko jinsin abin da zai fito din..
AMSA: Wannan irin kiyasin shi ne malamai suke kira da “kiyasun ma’al fãriq”, ba kuma a amfani da shi.. Sannan kuma shi din ne dai malaman Usulul fiqh suke kira da “Kiyasus Suriy” da yafi sauran nau’o’in kiyasi rauni..
FAHIMTAR DA TA FI KARFI:
Bayan kawo hujjojin duka bangarori biyu, a nan muna ganin masu cewa uwar ainihi a Shari’ance ita ce wadda ta dauki jaririn a mahaifarta, ta kuma sha wahalhalun ciki da haihuwa; saboda karfin dalilan da suka dogara da su, da kuma raunin dalilan masu daya fahimtar..
Allah shi ne masani na hakika.
Was Salamu alaikum.
© TASKAR SUNNA
No comments:
Post a Comment