A Kasar Japan wani mutum-mutumi mai aiki da na'ura mai kwakwalwa zai tsaya takarar gwamnan wata jiha.
Tuni aka fara lika hotunan dan takarar a wasu wurare tare da raba takardun hannu da ke dauke da manufofinsa.
Domin samun nasarar mutum-mutumin dole ne sai Michihito Matsuda da ya yi takarar gwamnan Tama a shekarar 2014 ya yi nasara.
Wato hakan na nufin idan Michihito Matsuda ya yi nasarar zabe, mutum-mutumi ne zai yi shugabanci ba shi ba.
Michihito Matsuda ya bayyana cewa, wannan ne karo na farko da dan adam ya samar da wannan fasaha kuma ya bude ofishin yakin neman zabe da shafin yanar gizo don tafiyar mutum-mutumin ta siyasa.
Matsuda ya yi wa 'yan jaridun Japan bayani game da wannan abı inda ya ce, bayanan da suke hannunsu na nuna cewa, mutum-mutumin ya fi mutane kaifin basira da tunani kuma zai iya shugabancin yankin sosai tare da yin aiyuka masu kyau na ci gaba.
No comments:
Post a Comment