Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Thursday, May 10, 2018

‘YAN HAKIKA DA ‘YAN IZALA DA MASU BOYAYYUN MANUFOFI... KU SAURARA … -01-


Dr Saleh Kaura :

BismilLahir Rahmanir Rahim..

Shimfida:

Babu shakka taron da Tijanawa "AhlulLahi" suke yi a duk shekara; domin tunawa gami da nazarin rayuwar Sheikhul Islam Maulana Sheikh Ibrahim Bn Alhaji Abdullah Niass (RadhiyalLahu Anhu) abu ne da yake d’aga hankalin mutane da kungiyoyin da a gaba dayan rayuwarsu suka sha alwashin ganin sun yaki wannan bawan Allah da duk abin da suka mallaka, musamman ganin irin miliyoyin mutane da suke taruwa; domin wannan munasabar, bugu da kari kuma, na wannan shekara ya zo da abin da ba su zata ba.. Ta yiwu haka ne ma ya sanya a wannan karo suka fito da dukan makamansu na kage da yarfe da karerayi; domin su bata wannan babban bawan Allah da ya karar da rayuwarsu wajen kora bayi zuwa ga soyayyar Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da kuma yi wa Allah bauta a matsayinsa na mahalicci mai azurtawa..

A gefe daya kuma, ga ‘yan hakika na karya, da suke karyar danganta kansu da Shehu Ibrahim Niass (RadhiyalLahu Anhu), wadanda su ma ba sa bayyana a tsawon shekara, sai lokacin wannan taro na Tijanawa ya karato!! Duka wadannan abubuwa ne da suke haifar da alamomin tambaya game da dalilan bayyanarsu a irin wannan lokaci, da kuma buyarsu a tsawon sauran watannin shekara!!..

Ga kuma wasu da suka dauki matakin yin adawa ta bangare daya, da suka keto ta tsakiyar wannan fitina; domin biya wa kai bukatu...., da sauran masu boyayyun manufofi..

******

Rudun da wasu suke fadi kuma suke rubutawa -a ‘yan kwanakin nan- na danganta Sufanci da Palsapar “Wahdatul Wujud” abu ne da yake kara tabbatar mana da cewa: lallai siyan manyan littafan addinin Musulunci a kasuwa, a kulle kai a daki a karanta su, ba tare da jagora, ko a gaban malami masani ba, hatsari ne babba da yake fuskantar ilimin Musulunci, da ma Musulman baki daya, musamman litattafan da aka yi su da harshen ilimi, a fagage irinsu: Fiqhu, da Usuluddeen da kuma Tasawwuf da sauransu..

Watannin baya, wani cikin masu yi wa ilimi dibar karan mahaukaciya ya bude littafin “Jawãhirul Ma’ãniy” na Sayyidi Sheikh Aliyu Harazumi al-Barada, ba tare da jagora ba, sai ya fito da wani abu na ban mamaki, inda yake riya cewa Shehu Ahmad Bn Muhammad Tijani (RadhiyalLahu Anhu) yana da akidar “Wahdatul wujud”!!..

Na ba shi amsa a lokacin, inda rashin fahimtarsa da maganganun Shehu (RadhiyalLahu Anhu) ya fito fili, da ma can fa sunan littafin da ya dauko wannan jawabin daga ciki: “Jawãhirul Ma’ãniy”, ma’ana “Gwala-gwalan Ma’anoni”, shi kuma “Gwal” a na samunsa ne a karkashin teku, ba kuma kowane “dan su” da mai ninkaya ne suke iya cim masa ba, sai kwararrun masana da suka kai wani matsayi a fannin ninkaya ta ilimi.. Babu shakka idan wasu sun kutsa cikin teku sun samo gwala-gwalai da daimon; sakamakon sanin makaman aiki, to, wasu idan suka shiga babu abin da za su samo sai tabo, da kwadi..

Magana akan “Wahdatul wujud” da “wahdatus Shuhud” tana bukatar wani mataki na ilimi, ba karatu ne da ake yi masa kwashi kwaraf, ko dibar karan mahaukaciya ba, karatu ne da yake da zurfi, kana kuma yana bukatar natsuwa, domin bambance tsakanin zare da abawa..

Amma tun da wadannan ‘yan ba ni na iya suka lafto wannan batu a cikin social media da sauran kafafen yada bayanai, suka kuma sanya shubuha a cikin zukatan mutanen da suke bibiyansu –da kyakkyawar niyya-, to ya zama dole mu yi duk abin da za mu iya, wajen saukake wannan batu ta yanda su kansu za su fahimci cewa kwadi suka kamo a cikin wannan shiga teku da suka yi, masu bibiyansu ma su gane cewa ba su kama reshe ba, ganye suka rike..

Saboda haka, a bayani mai zuwa za mu rarrabe tsakanin wadannan abubuwa daidai da yanda za a iya fahimta, kana kuma za mu biyo su da amsoshin wasu tambayoyi da Malam Abu Ahmad Ateeq ya yi mana, yana mai neman karin haske akan wasu daga cikin maganganun Shehu Tijani (RadhiyalLahu Anhu) da na Shehu Ibrahim Niass (RadhiyalLahu Anhu) Insha Allah..

Za a cigaba da ikon Allah

Saleh Kaura

©TASKAR SUNNA

No comments:

Post a Comment