Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Wednesday, April 18, 2018

Majalisar Dattawan Najeriya ta ba jami'an tsaron kasar umarnin nemo sandarsu cikin awanni 24


Majalisar Dattawan Najeriya ta bayar da umarni ga rundunar 'yan sandan Kasar da jami'an tsaro na farin kaya (SSS) da su nemo musu Sandarsu ta Majalisa wadda wasu da ba a gama tantance ko su waye ba suka kutsa kai tare da yin awon gaba da ita a safiyar Larabar nan.
A yayin zaman da Majalisar ta Dattawa ta yi ta karbi bakuncin takwarorinta na majalisar wakilai wadanda shugaban masu rinjaye na majalisar Femi Gbajamiala ya wakilta don nuna goyon baya ga 'yan majalisar dattawa.
Da ya ke neman ra'ayin 'yan majalisar, mukaddashin shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweremadu ya bayar da umarni ga rundunar 'yan sandan Najeriya da jami'an tsaro na farin kaya da nemo musu sandarsu cikin awanni 24 inda dukkan 'yan majalisar suka ce sun amince ta hanyar daga murya.
Sanata Ikweremadu ya kuma ce, maharan sun yi yunkurin yin garluwa da wasu mambobin majalisar ta dattawa 2 amma ba su yi nasara ba.
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya dai na takun saka da wasu mambobinta masu goyon bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
A kwanakin baya ne majalisar ta dakatar da Sanata Ovie Omo-Agege.

No comments:

Post a Comment