Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Kano da ke arewacin kasar, karo na biyu tun da ya zama shugaban kasa.
Shugaban
ya je Kano ne domin halartar daurin auren Fatima, 'yar gidan Gwamna
Abdullahi Umar Ganduje da Idris, dan gidan Gwamna Abiola Ajimobi na
jihar Oyo.Kano ita ce cibiyar siyasar shugaban kasar kuma a can ne ya samu kuri'ar da ta fi ta kowacce jiha a zaben shugaban kasa na shekarar 2015 inda ya kayar da Shugaba mai-ci Goodluck Jonathan.
A watan Disambar 2017 ne Shugaba Buhari ya kai ziyara jihar ta Kano karon farko tun da ya zama shugaban kasa.
A wancan lokacin, ra'ayoyin mazauna jihar sun sha bamban kan ziyarar ta shugaban kasar.
Wasu sun soke shi saboda abin da suka kira rashin kai ziyara duk da iftila'in da suka fuskanta a wasu kasuwannin jihar da rasuwar da wasu jiga-jigan 'yan jihar suka yi da kuma rashin gudanar da ayyukan ci gaban kasa a jihar.
Sai dai magoya bayansa sun yi murna sosai inda suka ce shugaban ya tabbatar da tsaro sakamakon yakin da yake fafatawa da masu tayar da kayar bayan kungiyar Boko Haram, daya daga cikin manyan alkawuran da ya sha alwashin tunkara a lokacin yakin neman zabe.
Bayan ziyarar da Shugaba Buhari ya kai Kano ne gwamnatinsa ta bayar da kwangilar gina hanyar Abuja-Kaduna-Kano wadda rashin bayar da kwangilar gina ta ta janyo wa gwamnatinsa suka, ko da yake har yanzu ba a soma aikin hanyar ba.
'Shugaban yana shan suka'
Sai dai wannan ziyara da Shugaba Buhari ya kai jihar ta Kano ta jawo masa cacaka a shafukan sada zumunta.
Masu amfani da shafukan sun ce shugaban kasar ba shi da dattako kasancewa bai kai ziyarar jaje ga jihohi irinsu Benue inda mutane da dama suka rasa rayukansu sakamakon rikicin da aka yi tsakanin makiyaya da manoma.
Kazalika, ya kai ziyarar ce a daidai lokacin da mazauna garin Dapchi ke ci gaba da zaman zulumin da suke yi sakamakon sace 'ya'yansu 110 da ake zargin mayakan Boko Haram sun yi amma shugaban bai je can ba.
Kazalika Shugaba Buhari ya ziyarci Kano ne bayan ya nada wani jigo a APC, Bola Ahmed Tinubu domin sasanta rikicin da ke faruwa a cikin jam'iyyar, ciki har da wanda ke faruwa tsakanin tsohon gwamnan jihar ta Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da Gwamna Ganduje.
Masana na ganin rashin jituwa tsakanin Kwankwaso da Ganduje ka iya yin mummunan tasiri wurin sake zaben Shugaba Buhari idan ya sake tsayawa takara a 2019.
No comments:
Post a Comment