Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Wednesday, April 18, 2018

An fara karbar takardun daliban kasashen waje don samun tallafin karatun digiri na farko a Turkiyya



Hukumar Bayar da Tallafin Karatu ta Turkiyya YTB ta fara karbar takardu daga daliban kasashen waje domin samun tallafin yin karatun digiri na farko a fannoni daban-daban.
An fara karbar takardun daga ranar 16 ga Afrilu kuma za a rufe a ranar 14 ga watan Mayu mai zuwa.
Daliban da suke son neman tallafin sai su tura takardunsu ta shafin yanar gizon Hukumar kamar haka: https://www.turkiyeburslari.gov.tr/en/english-home/
Turkiyya dai na ba wa dubunnan daliban kasashen duniya tallafin karatu a matakai daban-daban a kowacce shekara.
A yanzu akwai daliban kasashen waje sama da dubu 16 da suke karatu a Turkiyya a karkashin tallafin gwamnatin Kasar.

No comments:

Post a Comment