Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Friday, February 9, 2018

TSARIN DA MUSULUNCI YA SHIMFIDA WAJEN MU’AMALA DA WADANDA BA MUSULMI BA (6)




Dr. Saleh Kaura:

BismilLãh.

Alhamdu lilLãh..

ZANCE ALKUR’ANI GAME DA WADANDA BA MUSULMAI BA:

A bayanin da ya gabata, mun tabo wasu ayoyi da suka yi magana akan irin kallon da Akur’ani Mai girma yake yi wa Ahlul kitabi (Yahudawa da Kiristoci) –akan hanyar mu ta bayyan irin tsarin da Musulunci ya shimfida wajen yin dangantaka da wadanda ba Musulmai ba-, a yau –insha Allah- za mu kawo ayoyin da suka yi magana ne akan tsarin zamantakewa da daukacin wadanda ba Musulmi ba, ayoyin da suka bayyana yanda ya wajaba a zauna da su, a halin zaman lafiya da lumana, da kuma yanda za a zauna da su idan sun dauri aniyar cutar da Musulmai saboda Musuluncinsu....

******

Alkur’ani Mai girma ya hana Musulmai tsokanar wadanda ba Musulmai, ya hana cin mutunci, ko zagin abubuwan da wadanda ba Musulmai suke girmamawa, ko suke bautawa, Allah Madaukakin Sarki yana fadi a cikin suratul An’am, cewa: ((Kada ku zagi wadanda suke bauta wa abin da ba Allah ba, balle har adawa ta kai su zuwa ga zagi Allah cikin rashin sani..)) [al-Anam: 108]..

A nan addinin Musulunci ya lura da irin yanda wadanda ba Musulmai ba suke ji da allolinsu, suke kuma girmama su ne, tun da kuwa suna ganin girmansu, to ya ku Musulmai ku sani cewa: kwata-kwata bai halatta ku muzanta abubuwan da wadanda ba Musulmai ba suke girmamawa, wannan abu ne da zai kiyaye rayuwar zamantakewa daga fadawa cikin rikicin addini da fadace-fadace, sannan kuma hakan zai sa ba ku zamo sanadiyyar zagin Allah Madaukakin Sarki, domin idan kun zagi allolinsu, suka kuma suka zagi Allah, to ku ne sanadi..

A wani wurin ma Alkur’ani Mai girma ya hana yin sa-in-sa da da Ahlul kitabi in ba a cikin abin da yafi kyau da dacewa ba, Allah Mai girma yana cewa: ((Kada ku yi sa-in-sa da Ahlul kitabi sai dai in da abin da yafi kyau da dacewa ne..)) [al-Ankabut: 46]

Lallai wannan karantarwa shi ne ya koya wa Musulmai salon mu’amala da wadanda ba Musulmai ba cikin hali na wayewa da mutunci, addinin Musulunci bai nuna wa Musulmi zagin allolin wasu da da’awar cewa ai allolin karya ne ba, saboda haka ne ba za ka taba ganin wani Musulmi na kirki yana zagi allolin wasu, ko ya zagi Annabawan da aka aiko masu ba, duk kuwa da irin yanda wasu wadanda ba Musulman ba suka kware wajen cin mutuncin Annabin Musulunci, da ma duk wani abu da yake da jibi da Musulunci, suna masu riya cewa wai suna aiki ne da ‘yancin fadin albarkacin baki! Sun mance cewa babu yanda za a yi abin da yake barazana ga zaman lafiyar duniya gami da nagartacciyar zamantakewa ya zamo ‘yanci.

Haka ma addinin Musulunci ya wajabta wa Musulmai yin adalci duk runtsi, kuma wannan adalci da aka wajabta masu ba wai a tsakanin su da ‘yan uwansu Musulmai kawai ba ne, har da wadanda ba Musulmai ba, dole ne Musulmai su zamo masu fararen zukata a cikin dukan mu’amalarsu da kowa, kada su yarda kiyayya ta yi tasiri a cikin mu’amalarsu, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: ((Ya ku wadanda kuka yi imani: ku yi matukar kiyayewa a wajen bayar da hakkokin Allah, ku kuma bayar da shaida a tsakanin mutane kaman yanda take cikin gaskiya, kada tsananin kiyayyar da kuke yi wa wasu mutane ta sanya ku nesanci gaskiya wajen yi masu adalci, a’a, ku lizimci adalci a koda yaushe, domin adalci ne hanya mafi kusanci da tsoron Allah da kuma nesantar fushinsa.)) [al-Ma’ida: 8]

Babu shakka irin wadannan karantarwa su ne za su dakile duk wani yunkuri na husuma da rikici da ake yi da sunan addini, saboda duk wani rikici yana farawa ne da jifa da bakar magana, gami da wulakanta akidar wasu, a karshe kuma ya kai zuwa ga daukan makami da kashe juna.

Saboda haka ne Musulunci ya gina ka’idojin mu’amala tsakanin Musulmai da wadanda ba Musulmai ba akan “ADALCI” da “KYAUTATAWA” a gare su, bai kuma yi togiya akan wasu ba, in ba wadanda suka zabi hanyar yakar Musulmai da zaluntarsu, kawai saboda suna addini ba, wadanda suka sha-alwashin muzguna wa Musulmai ta hanyar fitar da su daga gidajensu, to wadannan kam Musulunci ya bayar da umurnin kada a yi masu mu’amala sai ta hanyar da su ma suke yi wa Musulmai mu’amala, har sai sun kame ga barin zaluntar Musulmai, ayoyin suratul Mumtahana su ne suka tsara wannan hukuncin, Allah mai girma yana cewa: ((Allah ba ya hana ku girmama da sada zumuntanku da kãfiran da ba su yake ku ba, ba kuma su fitar da ku daga gidajenku ba, lallai Allah yana son masu kyautatawa da kuma sada zumunta. Allah kawai ya hana ku daukan wadanda suka yake ku; saboda su hana ku bin addininku, -suka kuma tilasta maku fita daga gidajenku- a matsayin mataimaka, duk wanda ya dauki wadannan a matsayin mataimaka, to lallai ya zalunci kansa)) [al-Mumtahana: 8-9].

Wadannan su ne dokokin zamantakewar Musulmai da wadanda ba Musulmai ba da Allah ya gindaya, Allah bai hana mu yin zumunci da su ba, bai kuma ce mu zauna zaman doya da manja tsakaninmu da su ba, matukar dai ba su ne suka yake mu saboda addininmu, ko suka tilasta mana barin gidajenmu, ko suka taimaka wa wadanda suke tsangwamar mu saboda Musuluncinmu ba, Allah bai hana mu yin dangantaka ta mutunta juna da zaman lafiya da su ba, sai dai idan su ne suka takale mu ta hanyar nuna mana kiyayyar da ta kai su ga su yake mu saboda addininmu, to, dole ne mu dauki matakin kare kai, da kuma bayar da kyakkyawan darasi a gare su, domin su kuri gaba.

Irin wannan tsari da Alkur’ani Mai girma ya shimfida wa Musulmai shi ne daukacin kasashen duniya suke amfani da shi wajen mu’amalarsu da masoyansu da makiyansu.

Imamus Suyudi a cikin littafinsa “ad-Durrul Mansur, (2/87)”, ya kawo Hadisi daga Sayyiduna Abdullahi Bn Abbas (Allah ya kara yarda da shi) cewa: wasu daga cikin Musulmai sun kasance suna da ‘yan uwa a cikin Bani Kuraiza da Banin Nadhir (dangogi ne na Yahudawa), su Musulman ne suke ciyar da su, suke kuma ba su sadaka, suna son su shiga Musulunci, sai Allah ya saukar da wannan ayar: ((Ya Annabi Muhammadu (SallalLãhu alaiHi wa ĂliHí wa sallam), lallai shiryatar da wadancan batattun, da sanya su a hanyar alhairi ba a hannunka yake ba, naka kawai shi ne isar da sako, Allah shi ne yake shiryatar da wanda ya so, shi kuwa abin da kuke bayarwa na taimakon waninku, amfaninsa ku ne zai dawo wa, Allah zai ba ku lada akai, wannan fa idan ba ku nufi komai ba wajen ciyarwar sai neman yardar Allah kenan, duk wani abu na alhairi da za ku ciyar ta wannan hanyar zai dawo zuwa gare ku, ladansa zai sadu da ku a cike ba tare da an tauye maku ba)) [al-Bakra: 272]

A nan Allah bai shardanta zamowarsu Musulmai da yi masu adalci gami da kyautata masu ba.

*****

Zai yi kyau kafin na rufe wannan babi –da muka kawo yanda Alkur’ani Mai girma ya tsara dangantakar Musulmai da wadanda ba Musulmai ba- mu kawo maganar Alkur’ani Mai girma akan JAHADI, ganin cewa wasu suna amfani da babin JAHADI wajen soke dukan dangantakar da Alkur’ani ya bayyana na kyautata zamantakewa da wadanda ba Musulmai ba, wato ayoyin da muka kawo kadan daga cikinsu a wannan bayani da muke yi.. Wasu kuma wadanda ba Musulmai ba suna kokarin tabbatar da abin da wadancan masu gurbataccen fahimta game da al’amarin jahadi suka tafi a kai.. Saboda haka, bayani mai zuwa zai tabo Jahadi ne kaman yanda Alkur’ani ya tsara insha Allah..

Was Salamu alaikum.



© TASKAR SUNNA

No comments:

Post a Comment