Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Saturday, January 6, 2018

TSARIN DA MUSULUNCI YA SHIMFIDA WAJEN MUA'AMALA DA WADANDA BA MUSULMIBA 2

Dr Saleh Kaura :

BismilLãh.

Alhamdu lilLãh..

Wa sallalLãhu alã Sayyidina RasulilLãh..

Wa’ala Alihi Wa Sahbihi waman wãlãh..

YANDA ALKUR’ANI MAI GIRMA YA YI MAGANA AKAN WADANDA BA MUSULMI BA

SHIMFIDA:

Kalmar “wadanda ba Musulmai ba”, kalma ce mai fadin gaske da take kunshe da nau’o’in mutane iri-iri, daidai da irin kusanci, ko nesan dangantar su da Musulunci gami da Musulmai, ka ga tabbas akwai bambanci tsakanin wadanda ba Musulmai ba da suke zaman lafiya da fahimta tare da Musulmai, idan muka gwada su da wadanda suke daukan makami da zimmar kawo karshen Musulunci da Musulmai.. akwai kuma wadanda su adawa da gaba suke yi da Musulunci da Musulmai, ba kuma tare da sun kai ga daukan makami ba.. wannan a bangaren zamantakewa kenan..

A wani bangaren kuma Musulunci ya bambance tsakanin wadanda ba Musulmai ba da suka yi imani da samuwar Allah, da kuma wadanda suke kore samuwarsa kwata-kwata, masu ganin addini a matsayin shirme.. su kansu masu imani da samuwar Allah din sun sha bamban a tsakaninsu, domin akwai mabiya addinan da Annabawan da suka gabaci Sayyiduna Rasulullahi (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) suka zo da su, kaman Yahudawa da Kiristoci, akwai kuma wadanda suke bin wasu tsare-tsare na ruhi da wasu mutane ne suka samar da su, ba tare da suna da wata dangantaka da wahayi daga Allah ba, kaman addinin Buza, da Komfoshiyanci da sauransu.

Saboda haka, ba abin mamaki ba ne idan addinin Musulunci ya rarrabe wadannan mutane ta hanyar sanya hanyoyi mabambanta da zai gina dagantaka tsakanin masu imani da Musulunci da wadanda ba su yi imani da Musulunci ba, kowa daidai da kusancinsa da Musulunci, ko nesancinsa.

Amma duk da haka akwai wuraren da Alkur’ani mai girma ya hade zance game da dan Adam, a mtasayinsa na dan Adam, ba tare da ya bambance masu addini da marasa addini ba, kawai dan Adam din Allah ya karrama.. Ina ganin kawo shi a farkon wadannan darussa zai bayar da ma’ana matuka.

Bayan haka kuma sai mu shiga inda aka fayyace tsakanin masu addini da wadanda suke ba su da addini kwata-kwata, daidai da nesansu, ko kusancinsu da addinin Musulunci.

 ZANCE ALKUR’ANI GAME DA DAN ADAM

1 - SUNNAR HALITTA:

Alkur’ani mai girma ya bayyana sunnar Allah Madaukakin Sarki na halittar mutane da sifofi mabambanta, fara tun daga launi zuwa harshe da addini da sauransu, abin da zai sanya a fahimci duk wani yunkuri na hade mutane akan wani abu guda daya, to tamkar yake da kokarin cika kwando da ruwa! Saboda hakan ya saba da sunnar Allah gami da hikimarsa ta halitta, koda hakan ba zai hana a yi kokarin kusanto da juna, ta hanyar cigaba da kokarin kira zuwa ga addinin gaskiya, a karkashin inuwar karantarwar Alkur’ani mai girma, ma’ana dai ta hanyar kokarin sanin juna, da tattaunawa gami da fahimtar juna da ya kamata ya kasance a tsakanin Bil’adama ba.

AllahMadaukakin Sarki ya fadi  a cikin Alkur’ani mai girma cewa: ((Da Ubangijinka ya ga dama da gaba dayan wadanda suke doron kasa sun yi imani... Shin kai tirsasa mutane za ka yi har sai zamo mumunai?)) [Yunus: 99], wannan aya ta nuna cewa lallai sabani a addini sunna ne daga cikin sunnonin da Allah ya yi halitta a kai, saboda haka, duk yunkuri na shafe wannan sunnar daidai yake da kokarin tabo sama da kara!..

A wani wurin kuma Allah ya yanke wa duk wani da zai yi kokarin hada mutane akan wani addini guda daya ne wahala, inda Allah ya bayyana cewa: ((Ba fa za su taba gushewa a rarrabe ba, in ba wadanda Ubangijinka ya tausaya masu, domin saboda haka ya halicce su..)) [Hud: 118].

Saboda haka, shi sabani, ko bambance-bambance sunna ce ta Ubangiji wadda Alkur'ani mai girma ya tabbatar da ayoyinsa bayyanannu.. Kuma hakan yana nufin a sami dangantaka tsakanin wadannan halittu, dangantakar da za ta yi daidai da dabi'ar wannan sabani da bambanci, kada su ci karo da juna, kada kuma su warware juna, domin hankali ba zai dauki a ce: wai Allah ya kaddara samun sabani a tsakanin mutane, sannan kuma ya ba su umurnin su ki juna, ta hanyar da ta saba da dabi'ar da Allah ya halicce su a kai ba, ko kuma ya umurce su da su yaki juna, ta hanyar da za ta saba da hikimar da ya halicce su a kai ba.. Ta nan ne fa addini Musulunci ya tabbatar da 'yancin zaban addini da akida, kuma lallai: ((Babu dole a cikin al'amarin shiga addini)), ((Wanda ya so ya yi imani, wanda kuma ya so ya kafirce..)), ((Shin yanzu tirsasa wa mutane za ka yi har sai sun yi imani?)) ((Da Allah ya ga dama da ya tattara su akan shiriya, kada ka zamo cikin jahilai.)), ((Kai ba mai yi masu dole ba ne)) da sauran ayoyi masu yawa da suke dauke da irin wannan ma'anar..

A nan ne kuma Alkur'ani mai girma ya bayyana dangantaka irin ta zamantakewa, da na kasa da kasa a Musulunci, domin a tabbatar da cewa lallai Allah ya halicci mutane cikin sabani da bambanci, ya kuma ba su 'yancin yin imani ko rashinsa, domin dangataka a tsakaninsu ta zamo dangantaka ce ta zaman lafiya, dangantaka ce ta "fahimtar juna da taimakekeniya" kaman yanda Alkur'ani ya tabbatar: ((Ya ku mutane, lallai mun halicce ku ne daga asali daya wanda dukanku kuke daidai da juna, wannan asali kuwa shi ne Annabi Adam da Hauwa'u (Alaihimas-Salãm), ta hanyar auratayya ne kuma muka mayar da ku al'ummomi masu yawa da kabilu mabambanta; domin ku san juna, ku kuma yi taimakekeniya a tsakaninku, lallai wanda ya fi matsayi a wurin Allah duniya da lahira shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah, tabbas ilimin Allah ya game komai, kwararre ne kuma wanda babu wani abu komin kankantarsa da zai buya masa a cikin dukan al'amurra.)) [al-Hujrat: 13].

Ayoyin Alkur’ani mai girma da suka tabbatar da irin wannan ma’anar suna da yawa, dukansu suna sabar wa kwakwalwar Musulmi ne da amsar mutanen da suke da sabanin addini da na launi da na jinsi tare da shi, kaman yanda suke kara bude masa kofofi masu yawa da zai yi kira zuwa ga Allah Madaukakin Sarki, ba tare da ya kudiri aniyar kawar da sauran addinai daga bayan kasa dungurungum ta hanyar mayar da kowa Musulmi ba..

2 - YANDA ALLAH YA RABA ARZIKI TSAKANIN MUTANE:

A wani sabon salo da shi ma yake kara tabbatar wa Musulmi cewa ba shi daya ne Allah ya halitta a bayan kasa ba, a’a akwai wasu da suke da bambanci da shi a addini, kuma kasancewarsa Musulmi mai bin Allah ba zai zamo sanadiyya na yi masa arziki shi daya a kyale sauran ba, za mu ga Allah Madaukakin Sarki ya kawo mana labarin addu’ar da Annabi Ibrahim (AlaiHs Salam) ya fuskanci Allah Madaukakin Sarki da shi lokacin da ya kammala ginin Ka’aba, yana rokon Allah, yana cewa: ((Ya Ubangiji, ka sanya wannan gari ya zamo amintacce, ka kuma azurta wadanda suka yi imani da Allah da ranar lahira daga cikin mazauna wannan garin da kayan marmari…)) [al-Bakra: 126].

Lallai Allah Madaukakin Sarki ya amsa wani sashe na wannan addu’ar, inda ya amintar da garin, ya kuma zuba arziki mai tarin yawa a ciki. Sai dai duk da haka, Allah ya bayyana wa Annabi Ibrahim (AlaiHis Salam) cewa: ((Wanda ma ya kafirce zan jiyar da shi dadin dan kankani (yana nufin arzikin duniya), a lahira kuma zan wajabta masa azabar wuta, tir da irin wannan makomar)) [al-Bakra: 126].

Ma’ana dai wadanda ba Musulmai ba su ma ba za su rasa nasu kaso na arzikin duniya ba, muddin sun yi hanyoyin da ake samunsu, ba zan hana su saboda kawai ba su zabi hanyar yin imani da ni ba, shi sakamakon rashin imani a lahira ake yin sa ba a duniya.

Lallai wannan bayani na Alkur'ani mai girma zai sanya mumini na gaskiya ya ji cewa, lallai ba shi daya ne a cikin wannan duniya ba, kuma Allah ne ya hukunta haka, don haka dolen sa ya girmama hukuncin Allah ya yarda da zaman tare da mutanen da suke da bambanci da shi a addini, sannan kuma dolensa ya fita ya nemi arzikinsa, domin Allah bai raba arziki a wannan duniyar akan ma'aunin imani ba..

Bari mu dakata da wadannan misalai guda biyu, domin a darasi na gaba za mu kawo irin yanda Alkur'ani Mai girma ya yi magana ne akan wadanda ba Musulmi ba cikin Ahlul kitabi..



© TASKAR SUNNA

No comments:

Post a Comment