Dr Saleh Kaura :
BismilLãh.
Alhamdu lilLãh..
Wa sallalLãhu alã Sayyidina RasulilLãh..
Wa’ala Alihi Wa Sahbihi waman wãlãh..
ZANCE ALKUR’ANI GAME DA AHLUL KITABI (1)
Allah Madaukakin Sarki ya yi maganganu masu yawa game da wadanda ba Musulmi ba, ya kira su zuwa ga addini, ya kuma bayyana tsarin zama da su idan ba su amshi addini ba, -babu shakka- wadanda Alkur’ani ya fi ware zance na musamman akansu su ne “Ahlul kitabi”, wato Yahudawa da Kiristoci, saboda akwai dangantaka mai karfi tsakanin asalin addininsu da addinin Musulunci, abin da hakan ne kuma zai wajabta masu yin aiki da abin da yake cikin litattafan da aka saukar masu.
Lallai Alkur’ani mai girma ya kawo bayanin gurbatattun akidun Ahlul kitabi game da Allah, wanda ya zama dole a sifanta shi da duk wata sifa ta kamala, irinsu: ilimi, da iko, da rayuwa, da rashin kama, da sauran sifofin da suka dace da Ubangijin da yake halitta, yake kuma sanya-ido a cikin dukanin abubuwan da suka bayyana, da wadanda suka boye, Ubangijin da shi ne ainihin mai taikako, kuma shi ne zai yi wa bayi hisabi a lokacin da suka koma zuwa gare shi.
Duka wadannan bayanai sun zo ne a tsanake cikin hikima, da azanci, da kuma gwama hujja da hujja, babu zagi, babu cin-mutunci ko hauragiya ko kadan, saboda duk wanda ya gaji akida karkatacciya, to kuwa lallai ta’amuli da shi yana bukatar bi sannu a hankali, kafin har ya iya fahimtar haka, zagi da cin mutunci ba za su kara komai ba a nan in ba kara riko da abin da yake a kai ba, adalci shi ne babban kofar da ake shiga cikin zuciyar dan Adam, saboda haka ne za mu ga:
1 - Alkur’ani ya yi magana mai yawa akan Yahudawa da Kiristoci, fara tun daga tarihinsu, da kuma farkon samuwar addininsu, da kuma irin kalubalen da addinin ya samu a wurinsu. Duka wannan zance da Alkur’ani ya yi a kansu, ya yi su ne a kan adalci; (wato ajiye komai a wurinsa na asali), saboda haka lokacin da Alkur’ani Mai girma zai yi magana akan sifofin “amana” da “ha’inci” da a cikinsu, ya bayyana cewa lallai a cikinsu akwai wadanda suka kai matuka wajen kiyaye amana, kaman yanda akwai kuma wadanda suka kai matuka wajen ha’inci, Allah yana cewa: ((A cikin su akwai wanda idan ka amince masa akan wani adadi na zinare, ko azurfa, zai ba ka kayanka ba tare da wani abu ya tawaya daga cikin sa ba. A cikin su kuma akwai wanda idan ka amince masa akan dinare daya kacal, ba zai dawo maka da shi ba, sai idan ka matsa masa ka ba shi kunya)) [Ali Imran: 75].
2 - Haka ma bayan Allah Madaukakin Sarki ya ambaci irin zaluncin da wasu daga cikin Ahlul kitabi suka yi wa Annabawa, sai ya ce: ((Lallai ba duka Ahlul-Kitabi ne suke a matsayi daya ba, a cikin su akwai jama'an da suke akan hanya madaidaiciya, suna karanta littafin Allah a wasu sa'o'i na dare da rana a lokacin da suke sallah, ba sa bauta wa kowa sai Allah. Suna kuma gasgata samuwarsa da kadaitakarsa, kamar yanda suke gasgata Annabawa, da kuma zuwan ranar alkiyama, suna kuma bayar da umurnin aikata da'a da biyayya, suna hana sabo, suna kuma rige-rige wajen aikata alhairi, lallai wadannan a wurin Allah suna cikin salihan bayi..)) [Ali Imran: 113-114].
Wannan dalili daya ne daga cikin dalilan da ya sanya wasu daga cikinsu suka Musulunta, suka kuma kyautata Musulunci tare da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam)..
3 - Hakazalika Alkur’ani Mai girma ya yi nuni zuwa ga zancen nesanci, ko kusanci da wadanda ba Musulmi ba cikin Al hlul kitabi suke da shi da masu imani a cikin suratul Ma’ida, kana kuma ya yi magana akan malaman Kiristoci, da masu bautan cikinsu da suka yi riko da tafarkin Annabi Isah (AlaiHis salam), Allah mai girma yana cewa: ((Lallai za ka tarar da wadanda suka fi tsananin adawa da muminai su ne: Yahudawa da Mushrikai.. Kuma za ka tarar da wadanda suka fi kusanci wajen nuna soyayya ga muminai su ne: wadanda suka ce su Kiristoci ne, wannan kuwa ya kasance ne saboda a cikinsu akwai malamai da masu bauta, kuma tabbas ba sa yin girman-kai. Idan sun saurari abin da aka saukar wa Manzon Allah, za ka ga idanuwansu suna kwararar da hawaye; sakamakon gaskiyar da suka sani, suna cewa: Ya Ubangijinmu lallai mun yi imani, saboda haka ka rubuta mu cikin masu shaidawa)) [al-Ma’ida: 82-83].
Babu inda Ahlul kitabi za su sami irin wannan adalci da Alkur’ani Mai girma ya yi masu in ba a karkashin inuwar Musulunci ba, adalcin da yake nuna cewa lallai a cikin su akwai wadanda suka bi tafarkin da Annabawansu suka bar su a kai, suka kuma rike wannan tafarkin gam, kaman yanda akwai kuma wadanda suka kauce suka yi wa son zuciyarsu biyayya..
****
Kasancewar wannan maudhu’in -na bayanin Alkur’ani mai girma game da Ahlul kitabi- maudhu’i ne mai fadin gaske, zan cigaba da kawo shi a rubutu na gaba idan Allah ya yarda..
© TASKAR SUNNA

No comments:
Post a Comment