Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Saturday, January 6, 2018

TSARIN DA MUSULUNCI YA SHIMFIDA WAJEN MU'AMALA DA WANDA BA MUSULMI BA 1

Dr Saleh Kaura :

BismilLãh.

Alhamdu lilLãh..

Wa sallalLãhu alã Sayyidina RasulilLãh..

Wa’ala Alihi Wa Sahbihi waman wãlãh..

Babu shakka addinin Musulunci addini ne -da tun farko- ya tsara yanda ya kamata rayuwar zamantakewa ta kasance tsakanin Musulmai da suka yi imani da shi, da wadanda ba Musulmai ba, kuma wannan tsarin ya zartu a aikace a cikin rayuwar Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam). Inda aka yi rayuwa cikin mutunta juna da kuma kokarin fahimtar juna, tsakanin Musulmai da wadanda ba Musulmi ba a garin Madina, lallai garin Madina yana kunshe ne da mutane mabambanta a addini; domin akwai: Musulmai na garin da wadanda suka yi hijira zuwa zuwa garin, da kuma wadanda ba Musulmai ba cikin Larabawan garin, ga kuma Yahudawa da suka zauna a garin na tsawon lokaci, farkon “kundin tsarin zamantakewar” da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) ya samar a wannan garin babban dalili ne akan abin da muka ambata..

Sai dai duk da haka, wasu sun dage sai sun fahimci duk wani kira na maimaita irin wannan rayuwar a matsayin kokarin cakuda addinai, ta yanda za a kawar da dukan bambance- bambance na imani da ayyuka! Wannan kam rashin fahimtar inda aka dosa ne, da kuma kokarin kawo rudani a cikin kasar da ake zaman-tare da wadanda ba Musulmi ba.. ta yiwu dalilin su na yin haka bai rasa nasaba da irin yanda suka dage sai sun fahimci addini da fahimtar wata kasa da a cikinta kaf babu wanda ba Musulmi ba, mutum a kasa kaman Saudiyya –alal misali- zai iya kare rayuwarsa kaf ba tare da ya yi tozali da Kirista ko Bayahude ba, don haka, ba zai yiwu a dauko tunaninsa na zamantakewa a kawo kasa kamar Najeriya a ce za a yi aiki da ita ba, domin fatawarsa ta yi daidai ne –wata kila- da kasarsa..

Babu shakka a lokacin da malaman Najeriya suke yin ijitihadi –cikin abubuwan da Musulunci ya yarda a yi ijitihadi akansu- sun iya samar da kyakkyawan yanayi na zamantakewa tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi ba, karkashin fatawowin da suke lura da wuri gami da lokaci “az-Zamãn wal Makãn”, da kuma abubuwan da za su je su dawo “Fiqhul ma’ãlat”, da ma abubuwan da suka faru sababbi “Fiqhun Nawãzil” da sauransu.. Sai dai lokacin da wasu suka dauko salon “copy & paste” a cikin al’amarin zamantakewa na addini, suka kwafo tsari daga wurin da rayuwarsu ta saba da tamu, al’adunsa suka sha bamban da namu, sai abubuwa suka dagule, zaman-doya da manja ya zamo shi ne sarki a tsakanin su kansu Musulmin da junansu, ba ma wai tsakaninsu da wadanda ba Musulmai kawai ba..

Bugu da kari, akwai wasu da suka kuduri aniyar killace addinin Musulunci a wuraren da yake, ta hanyar sanya masa tarnakin da zai hana shi cirawa zuwa kasashensu, musamman sun ga irin yanda mutanensu suke amsar wannan addinin ba dare ba rana, domin yana dauke da amsoshin tambayoyinsu masu tarin yawa a cikin rayuwarsu ta gangan jiki, da rayuwarsu ta ruhi.. sai suka kirkiri hanyoyin da za su bakanta wannan addinin a idanuwan mutanensu, sai kuwa suka shigo wa addinin Musulunci daka-da-kare ta hanyar masu tsattauran ra’ayi, daga nan sai aka haifar da wani haramtaccen d’a da addinin Musulunci bai taba saninsa a cikin tsarinsa ba, hasali ma ya zo ne domin ya nesanta halitta daga sharrin ta’addanci da ‘yan ta’adda.

Da haka ne wadancan makiran suke ganin sun nesantar da mutanensu daga shiga addinin da masu danganta kansu da shi ba su girmama mutuntakar wanda ba shi a cikinsu, su ne saka bama-bamai da nakiyoyi a Coci-coci da Masallatai da kasuwanni da duk wani wuri na taruwar dan Adam, kuma wai da sunan addini!!

Wadannan dalilan –da su ne ummul haba’isin tashin hankali, da rashin jituwar da suke faruwa a kasarmu- su ne suka sanya ni ganin muhimmanci na bude wannan babin, domin bayyana irin yanda addinin Musulunci ya shata dangantaka tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi ba..

Ina fatan wannan rubutun ya tabo:

1- Yanda Alkur’ani Mai Girma ya yi magana akan Wadanda ba Musulmi ba.

2- Yanda Annabi (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) Ya gabatar da rayuwarsa da Wadanda ba Musulmi ba a aikace.

3- Rayuwar Sahabbai da wadanda ba Musulmi ba.

4- Yanda malaman Fiqhu suka bayyana irin yanda rayuwar zamantakewa take tsakanin Musulmi da waninsu

5- Cigaban da aka samu sakamakon kyautata zamantakewa da wadanda ba Musulmi ba.

6- Yanda dangantakar Musulmi da wadanda ba Musulmi take a wannan zamanin.

Ba na jin cewa zan iya karade komai da komai game da wannan maudhu’in, saboda haka aiki na ba zai wuce nuni gami da share fage ga masu karatu domin su fadada bincike ba, Allah nake rokon ya datar da mu baki daya wajen aza harsashen rayuwa akan inda ya bayar da umurni, ya kuma sanya mu nesanci abubuwan da za su kawar da mu ga barin hanyarsa, Allahumma amin.

Saleh Kaura

© TASKAR SUNNA

No comments:

Post a Comment