Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Wednesday, January 10, 2018

TSARIN DA MUSULUNCI YA SHIMFIDA WAJEN MU’AMALA DA WADANDA BA MUSULMI BA (4)


Dr Saleh Kaura :


BismilLãh.

Alhamdu lilLãh..

Wa sallalLãhu alã Sayyidina RasulilLãh..

Wa’ala Alihi Wa Sahbihi waman wãlãh..

Idan ba mu manta ba, a bayanin da ya gabata muna cikin kawo bayanin Alkur’ani mai girma ne game da Ahlul Kitabi, wato Yahudawa da Kiristoci, kaman yanda muka fadi cewa bayanin yana da yawa, to yanzu za mu cigaba da kawowa amma a takaice insha Allah…

ZANCE ALKUR’ANI GAME DA AHLUL KITABI (2)

Alkur’ani mai girma ya sanya imani da dukan Annabawan da suka gabaci Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) sharadi ne, ko mu ce: ginshiki ne mai girma a cikin imanin daukacin Musulumi, Mai girma da dauka yana fadi a cikin suratul Bakra cewa: ((Dukansu –Manzon Allah, da muminai- sun yi imani da Allah, sun kuma yi imani da mala’ikunsa, sun kuma yi imani da litattafansa, sun kuma yi imani da Manzanninsa, suna daidaita tsakanin Manzannin Allah wajen imani da su, da girmama su,)) [al-Bakra: 285].. irin wannan ma’anar ce ma za ka tarar a aya ta 126 a cikin wannan sura; saboda su ((Annabawa tamakar ‘ya’yan uba daya ne, a iyayensu mata ne kawai suka bambanta, amma addininsu daya ne)) [Muslim].

Alkur’ani bai tsaya kawai akan wajabta wa Musulmai imani da Annabawan da suka gabaci Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) ba, a’a ya bibiye ayyukan rashin ladabi da cutarwar da wasu mabiya addinai suka yi wa Annabawansu da ma Annabawan wasunsu, ya shimfada bargon “Isma” ga daukacin Annabawa, bargon da zai zamo kariya a gare su ga barin duk wani aikin sabo da aka danganta masu, ko wata cutarwa da aka yi masu, alal misali: Alkur’ani ya bai wa Annabi Musa (AlaiHis salam) kariya akan cutarwar da Yahudawa suka yi masa, Allah mai girma yana cewa: ((Ya ku wadanda kuka yi imani, kada ku kuskura ku zamo tamkar wadanda suka cutar da Annabi Musa, Lallai Allah ya wanke shi ga barin abubuwan da suka fada, lallai shi din yana da babban matsayi a wurin Allah)) [al-Ahzab: 69].

Haka ma Alkur’ani mai girma ya bai wa Sayyida Maryam ‘yar Imran (AlaiHas salam) kariyar da ta tabbatar da tsarkinta gami da kamewarta, inda Allah ya bayyana matsayinta da karamarta a wurin Allah, Mai girma da daukaka yana cewa: ((Duk sanda Annabi Zakariyya (AlaiHis-Salãm) ya shiga wajen da take bauta, sai ya sami kayayyaki na marmarin da ba lokacin su ne ba, sai ya ce- yana cike da mamaki- ya Maryam, ina kika sami wannan arzikin? Sai ta ce: Ai wannan kadan ne cikin falalar Allah…)) [Ali Imran: 37].

Alkur’ani mai girma a wata ayar kuma ya bayyana irin kame-kai da kuma zabin da Allah ya yi mata, Allah yana cewa: ((Ya kai wannan Annabi (SallalLãhu alaiHi wa ĂliHí wa sallam), fada masu lokacin da mala’iku suka ce: ya sayyida Maryam (AlaiHas-Salãm), lallai Allah ya zabe ki; domin ki zamo mahaifiyar Annabinsa, ya kuma tsarkake ki ga barin dukan kazanta, inda ya kebance ki –da zama mahaifiyar Annabi Isah (AlaiHis-Salãm)- da falala akan dukan halittu.)) [Ali Imran: 42].

Haka ma Akur’ani mai girma ya kawo karshen husumar da ta-ki-ci, ta-ki-cinyewa tsakanin Yahudawa da Kiristoci, inda Kiristoci suke tuhumar Yahudawa da kashe Annabi Isah (AlaiHis Salam), sai Allah ya raba masu gardama da cewa: ((Gaskiyar al’amari shi ne, ba su kashe shi kaman yanda suka riya ba, ba kuma su tsire shi kaman yanda suka yi da’awa ba.. kawai dai an kamanta wani da shi ne, sai suka zaci cewa sun kashe shi, sun kuma tsire shi.. a’a, sun dai kashe da tsire wanda ya yi kama da shi ne.. Lallai tun a lokacin sun yi ta sabani a tsakaninsu: shin Annabi Isah (AlaiHis Salam) suka kashe, ko kuwa waninsa? Dukansu suna shakka akan al’amarinsa..)) [an-Nisa’i: 157].

Da haka Alkur’ani mai girma ya bayyana gaskiya game da babban dalilin sabani tsakanin Yahudawa da Kiristoci, abin da ya sanya wasu daga cikin manyan Coci-coci suka dawo suka sake nazari game da al’amarin, har suka sake gina dangantaka mai kyau tsakaninsu da Yahudawa, domin Alkur’ani mai girma ya wanke Yahudawa daga zargin kashe Annabi Isah (AlaiHis salam); kawai kasancewa Kiristoci sun gina akidarsu akan mas’alar “Tsirewa” shi ya sanya har yanzu ba a dawo gaba daya daga rakiyar wannan batu ba, sai dai duk haka, hakan ya sanya a manna kisan zuwa ga wani da ba a san ko wane ne ba.

Za mu iya cewa lallai Alkur’ani mai girma ya kawo tarihi tsaftatacce na Annabawan Allah, domin shi ne ingantaccen littafin da ya yi bayani akan manyan Annabawa, ya bayyana yanda aka haifi wasu daga cikinsu, ya kuma nuna irin yanda ya zabi wasunsu, ya kuma yi magana akan hakuri gami da juriyarsu a cikin wahalhalun da suka fuskanta a kan hanyarsu ta kira zuwa ga Allah Madaukakin Sarki.

Ya isa mu gane haka ta inda Alkur’ani Mai girma ya ambaci suna Annabi Musa (AlaiHis salam) karara har sau 136, ya kuma ambace shi da sifofinsa sau 50.

Shi kuwa Annabi Isah (AlaiHis salam) sai da Alkur’ani mai girma ya ambace shi da sunansa sau 25, da sifofi irinsu: RuhulLah, KalimatulLah, Mubarakun, mai bin iyaye, sai da ya ambace shi a haka sau 20.

A nan Alkur’ani mai girma yana koyar da Musulmi ne hanyoyin da za su girmama daukacin Annabawa, su kuma mutunta su, hakan ne kuma ya sanya Musulmai ba sa wargi a duk abubuwan da suka shafi Annabawa, malaman Tauhidi da na Tafsiri sun yi rubutu mai yawa game da “Ismar” Annabawa.. mas’alar da take wanke dukanin Annabawan Allah daga soki-burutsun da aka danganta masu na karya, ko wani sabo..

Babu shakka girmama Annabawan da suka gabaci Sayyiduna RasululLahi (SallalLahi alaiHi wa alihi wa sallam) –musamman Annabawan Ahlul kitabi- shimfida ce mai kyau da za ta sanya dangataka tsakanin Musulmi da Ahlul kitabi ta yi kyau..

Zan cigaba da kawo ayoyin da suka yi magana akan wannan fagen insha Allah a bayani na gaba.


© TASKAR SUNNA

No comments:

Post a Comment