Jirgin yaki na sama mallakar Kawancen kasashen Larabawa da Saudiyya ke wa jagoranci ya fado a Kasar Yaman inda aka samu nasarar kubutar da matukansa 2.
Sanarwar da Kawancen kasashen Larabawar suka fitar ta ce, sakamakon matsala da jirgin ya samu ya fado a yankin lardin Sada.
Sanarwar ta ce, an kubutar da matukan jirgin 2 tare da kai su Saudiyya.
Tashar talabijin ta Al-Misra mallakar 'yan tawayen Houthi ta ce, harbo jirgin aka yi.
Tsawon shekaru ana rikicin siyasa a Yaman inda dakarun gwamnati da 'Yan tawayen Houthi suke arangama da juna.
A watan Maris din 2015 ne kuma gwamnatin Yaman ta nemi taimakon kasashen Larabawa domin yakar 'yan tawayen na Houthi.
No comments:
Post a Comment