Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Wednesday, January 10, 2018

An sayar da 'yan Najeriya 20 a matsayin bayi akan dala 735 kachal



Shugaban hukumar NEMA ta Najeriya Sulaiman Labaran ya bayyana cewar gwamnatin Najeriya ta maido da daruruwan 'yan gudun hijirar kasarta daga Libiya zuwa gida, inda ya tabbatar da an sayar da wa su 'yan kasar 20 amatsayin bayi da kudi dala 735.
Labaran ya kara da cewa wadanda aka sayar din ba'a iya tabbatar da  ko su na raye ko mace ba. A cewar sa ya kamata  gwamnatin Libiya ta dauki kwararan matakai akan lamarin saboda abinda mu ka ji daga bakunan wadanda su ka dawo gida daga libiyar babu dadin ji.
Labaran, ya shaidawa manema labarai da cewa 'yan gudun hijirar da ke kasar Libiya na cikin mawuyacin hali na rashin abinci, ruwan sha, a yayinda  mata daga cikin su ke fuskantar fade.
Sabili da kwararan matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka a cikin wata daya an dawo da 'yan gudun hijirar kasar da ke neman zuwa kasashen turai dubu 2 da 778.
A cewar ma'aikatar shige da fice ta Najeriya, a shekarar da ta gabata, 'yan gudun hijirar Najeriya 16,387 aka dawo da su gida daga kasashen  Libya, Italiya da Saudi Arabia.

A dalilan  cin hanci da rashawa da su ka yi katutu a kasar da kuma matsalolin tattalin arziki al'umar kasar Najeriya na fama  da matsalar tsadar rayuwa. Haka kuma fitinun da ke faruwa a wasu yankunan kasar sun sanya duban mutane barin gidajen su.
Da yawan wadanda ke sun isa kasashen turai amtsayin 'yan gudun hijira ka rasa rayukan su a hannun ma su cinikin bayi, a cikin hamada ko teku. 

No comments:

Post a Comment