Rundunar sojin Najeriya ta yi ikirarin ji wa shugaban wani bangare na kungiyar Boko Haram mummunan rauni a harin da dakarunta suka kai masa.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da manema labarai na rundunar saman da tsaro ta Operation Lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce, "Mamman Nur ya samu mummunan rauni sakamakon hari ta sama da rundunar ta kai musu."
"Shi da wasu kwamandoji kungiyar sun tsere, amma an kashe mayakansa da dama. Wasu daga cikin mayakan kungiyar da suka tsere sun mika wuya ga rundunar sojin Jamhuriyar Nijar bayan gwamnatin kasar ta yi afuwa ga wasu 'yan kungiyar", in ji sanarwar.
Sanarwar ta zo ne kwana kadan bayan daya shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da sabon bidiyo, wanda a cikinsa ya dauki alhakin hare-haren da aka kai a Maiduguri da Gamboru da Damboa.
Shekau ya musanta cewa an ci karfin 'yan kungiyar, yana mai cewa suna nan kalau cikin koshin lafiya.
A jawabin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na sabuwar shekara dai, ya ce dakarun kasar sun ci karfin 'yan Boko Haram.
Sai dai 'yan kungiyar na ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake.
No comments:
Post a Comment