Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Saturday, January 6, 2018

Ko Donald Trump yana da tabin kwakwalwa ?

An sha yin mahawara a kan ko Donald Trump na da tabin hankali - ko kuma kalau yake.
Muhawarar ta sake bullowa a shafukan sada zumunta kamar Twitter bayan da wani dan jarida da ke birnin New York ya wallafa wani sabon littafi.
Daya daga cikin manyan tuhumar da wasu ke yi masa, ita ce bai cancanci ya rike ofishin shugaban kasa ba saboda mai alfahari ne da ya wuce kima.
A halin yanzu mahawarar tana duba kaifin basirarsa domin ana ganin shekarunsa sun fara ja, ko kuma ya fara kamuwa da cutar mantuwa ne.

Me jama'a ke cewa?

Wannan mahawarar ta samo asali ne bayan da aka wallafa wani littafi mai suna Fire and Fury da wani dan jarida, Michael Wolff ya rubuta inda yake cewa a yayin da Mista Trump ke shirin shiga fadar White House ya lura cewa makarraban shugaba Trump sun gane "kaifin hankalinsa suna raguwa."
Mista Wolff ya wallafa wani rahoto a jaridar Hollywood Reporter cewa Mista Trump kan maimaita maganganu sau da yawa. Maimaita batu, alama ce ta kamuwa da cutar mantuwa wato dementia, wadda ke shafar kashi 5 zuwa 8 cikin dari na mutanen da suka haura shekara 60 da haihuwa a duniya, inji Hukumar Lafiya da Majalisar Dinkin Duniya.
Shekarun Mista Trump 71.
"Da farko ya kan maimaita maganar, kalma zuwa kalma na labarai uku da ya bayar a kowane minti 30 - amma yanzu lokacin ya ragu zuwa minti 10".
Amma Mista Wolff bai bayar da misali ba dangane da wannan ikirarin nasa.
Shi kuwa Mista Trump ya soki littafin, inda ya kira shi "jabu", wanda ke "cike da karya" kuma ya ce bai ba taba ba Mista Wolff izinin shiga fadar White House ba.

Likitoci masu nazarin halayyar dan adam sun taba bayyana cewa Mista Trump na da alamar tabin hankali.
An wallafa littafai game da wannan batun jim kadan bayan darewar MIsta Trump karagar mulki: LittafinBandy X Lee The Dangerous Case of Donald Trump; da Twilight of American Sanity na Allen Frances da kuma littafin Fantasyland wanda Kurt Andersen ya wallafa.
Dokta Lee wanda kwararren likitan nazarin halayyar dan adam ne a Jami'ar Yale, ya fada wa wasu sanatoci wadanda yawancinsu 'yan jam'iyyar demokrat ne a watan jiya cewa Mista Trump "zai zare, kuma mun fara ganin alamun."
Amma abin lura a nan shi ne babu wanda ya taba zama likitan Mista Trump a cikin wadannan mutanen, kuma basu da cikakken bayani game da lafiyar hankalinsa.
Wanda ya taba duba lafiyarsa ba zai iya bayyana abin da ya sani ba, domin yin hakan zai zama laifi a karkashin dokar Amurka da ta hana likitoci su bayyana halin lafiyar da wadanda suka duba suke ciki.

Me yasa aka damu da wannan batun?

A takaice Mista Trump na iya rasa aikinsa.
A karkashin gyarar doka ta 25 ta tsarin mulkin Amurka, idan shugaban kasa ya nuna alamun "gazawa wajen sauke nauyin aikin ofishinsa," mataimakin shugaban kasa ne zai karbi mulki. Amma wannan ba zai faru ba sai idan shi mataimakin shugaban kasar, tare da ministocin gwamnatin Mista Trump sun kaddamar da batun.
Yiwuwar haka abu ne mai wuya, amma mutane da dama sun fara kiraye-kirayen a yi hakan.

Ko an taba bin wannan hanyar?

Tabbas an taba - shugabannin Amurka sun sha samun matsalar tabin hankali, misali Abraham Lincoln wanda matsalar tabin hankali ta janyo sukurkucewar mulkinsa.
Sai kuma na baya-bayan nan Ronald Reagan, wanda yayi mulki daga 1981 zuwa 1989, inda ya taba fada wa halin rudewa, har ba ya iya tuna inda yake a wasu lokutan.
Bayan saukarsa daga mulki da shekara biyar, likitoci sun gano yana da cutar Alzheimer's mai sa mutum ya manta da abubuwa kuma ya rika rudewa.
Amma ba a taba amfani da gyaran doka ta 25 ta tsarin mulkin Amurka ba wajen tsige shugaban kasar mai ci.

To ina shaidar da ta alakanta Mista Trump da wannan cutar?

A baya dai wasu na ganin cewa Mista Trump na fama da cutar Narcissistic Personality Disorder (NPD) mai sa mutum ya rika ganin yafi kowa iya komai.
Mujallar Psychology Today ta ce masu fama da cutar na bayyana wasu daga cikin halayen nan:
  • Son kambama abubuwa, da rashin tausayawa sauran mutane da kuma son a yaba wa mutum a ko yaushe
  • Masu wannan matsalar na ganin sun fi kowa ko kuma sun cancanci a basu kulawa ta musamman
  • Su kan nemi a girmama musu matuka kuma suna son a kula da su, kana ba sa iya jure suka ko gazawa
Amma mutumin da ya rubuta wadannan bayanan game da cutar ta NPD, Allen Frances ya ce rashin bayyana rudani ne ya hana shi cewa Mista Trump na da wannan lalurar.
Ya rubuta cewa, "Mista Trump na zama sanadiyyar tashin hankali ga mutane a maimakon shi ne yake cikin tashin hankali, kuma akan yaba masa ne maimakon a soke shi a yayin da yake nuna rashin tausayi.
Amma a yanzu, mutane na ganin watakila Mista Trump na fama da tsufa ne kawai.
Sun nuna yadda ya kan maimaita kalamansa, kamar yadda Mista Wolff ya wallafa a cikin sabon littafinsa.
Ana ganin wannan alama ce ta cutar Alzheimer's, inji masana kiwon lafiya, ko kuma tsufa ce ta kama shi.

A makon gobe ne shugaban zai ga likita domin a duba lafiyarsa - amma lafiyar jikinsa kawai za a duba - a karon farko tun da ya zama shugaban kasa.

Yaya 'yan jam'iyyar Republican suke kallon wannan mahawarar?

Kakakin fadar White House, Sarah Huckabee Sanders ta ce: "Abin kunya ne, kuma abin dariya."
"Idan da ba shi da lafiya, da bai kai ga zama a kujerar ba, kuma da bai kada kwararrun 'yan takarar da jam'iyyar Republican ta taba fitarwa ba."
Amma wasu sun fi ta sukar lamarin.
Bayan da Jeb Bush ya bayyana cewa "mutumin na bukatar a duba lafiyar hankalinsa," a yayin da ake yakin neman zabe, wani sanata daga jihar Tennessee, Bob Corker cewa yayi a watan Agusta Mista Trump ba shi da "natsuwar" da ake bukata wajen shugabancin kasar.

No comments:

Post a Comment