Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Tuesday, January 9, 2018

Gwamnatin Iran ta hana koyar da darussan Turanci




Shugaban Majalisar Kula da Ilimi Mai Zurfi ta Iran Mehdi Navid Ethem ya bayyana cewa, koyar da darussan yaren Turanci a makarantun gwamnati da masu zaman kansu ya saba ba dokokin Kasar.
Ethem ya tattauna da wata tashar talabijin din Iran inda ya bayyana cewa, daga yanzu yaren Turanci ba ya daga cikin darussan da za a dinga koyarwa a makarantun kasar, kuma ba a yi wata tattaunawa ba kan bayar da dama a koyar da yaren Turanci a makarantu masu zaman kansu.
A gefe guda, an bayyana cewa, shugaban Addini na Iran Ali Khumaini ya ce,, koyar da yaren Turanci a kasar na ba wa kasashen yammacin duniya damar mamaye al'adun Iran.

No comments:

Post a Comment