Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Sunday, January 14, 2018

Gwamnatin Nigeria ta ki daukar mataki kan kisan Fulani 800 —Sarki Sanusi



Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce gwamnatin Najeriya ta ki daukar mataki a kan kisan da aka yi wa Fulani sama da 800 a jihar Taraba da ke arewacin kasar.


Sarkin na Kano ya tabbatarwa BBC cewa ya mika wa gwamnatin hotunan Fulani 800 - cikinsu har da mata da kananan yara - da aka kashe a jihar amma har yanzu babu matakin da aka dauka.
Yana wannan bayani ne a daidai lokacin da ake zargin Fulani makiyaya da kisan mutane da dama a jihohin Benue da Taraba, ko da yake sun musanta zargin.
Basaraken ya dora alhakin kashe-kashen da ke faruwa a jihohin a kan Fulani makiyaya da manoman jihohin, yana mai cewa ba a bayar da hakikanin yawan Fulanin da aka kashe inda ake nuna bangaranci.
Sarki Sanusi, wanda ya tabbatar da hirar da ya yi da jaridar Punch kan lamarin, ya ce, "A 'yan watannin da suka gabata a Mambilla, mayakan sa-kai na kabilun yankin sun kashe Fulani sama da 800. Babu jaridar da ta je can ballantana ta ba da labarin abin da ya faru."
A cewarsa, "Cikin mutanen da aka kashe har da wata mata mai ciki, wadda aka yanka cikin nata aka fito da jaririn sannan aka yanka shi. Da kaina na mika wa gwamnatin tarayya wani kundi dauke da sunaye da hotunan mutanen da aka kashe da adireshin mutanen da ake zargi da yin kisan."
Sarki Sanusi ya kuma ce, "Kazalika, sai da na tabbata cewa hukumomi sun karbi shaidun bidiyo da hotuna na manyan 'yan siyasar jihar Taraba wadanda ke da hannu a wannan kisa na kare-dangi. Amma babu wanda aka kama.
"An kashe Fulani a Kajuru [jihar Kaduna] da Numan [jihar Adamawa]. A lokuta da dama mayakan sa-kai ne kawai ke dirar wa Fulanin su kashe mata da 'ya'yansu".
Ya kara da cewa irin wannan rikicin ba zai kare ba idan ba a dauki mataki a kan mutanen da ke hadda su tun da farko ba.

No comments:

Post a Comment