Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Thursday, January 18, 2018

HUKUNCIN HAYAR MAHAIFA, DA SAYAR, KO KYAUTAR DA KWAYOYIN HALITTA A MUSULUNCI (4)


Dr Saleh Kaura :

A baya, mun bayyana ma’anar “Hayar mahaifa” da kuma ma’anar “Sayar, ko kyautar da kwayoyin halitta”, mun kuma kawo surori gami da nau’o’in kowanne, sannan muka kawo hukuncin Musulunci game da kowanne daga cikinsu –mai neman sanin haka zai iya komawa bayanai na 1- 2-  3-..

A yanzu –da ikon Allah- za mu kawo bayani gami da hukuncin idan hakan ya auku ne a aikace, wane za a danganta wa dan a matsayin uba? Kuma wace za a danganta wa dan a matsayin uwa?

Tabbas idan hakan ya riga ya faru –duk da cewa haramun ne kaman yanda muka bayyana-, har ya kai ga an sami da, an kuma haife shi, to babu shakka akwai bukatar sanin hakikanin uwa da uban wannan jariri, da wane za a danganta shi? Domin akwai hakkokinsa tun daga tarbiyya har zuwa gado, su ma iyayen suna da nasu hakkokin na zamansu iyaye.

WANE NE UBAN DAN DA AKA HAIFA TA WADANNAN HANYOYI?

A nan akwai abubuwa guda uku, ita matar da ta bayar da haya, ko kyautar mahaifar za ta iya zamowa matar shi mai maniyyin ce.. za kuma ta iya zamowa ba matarsa ba ce, idan ba matarsa ba ce, za ta iya zamowa matar wani ne daban, zai kuma iya zamowa ba ta da aure kwata-kwata.. kowanne daga cikin ukun nan yana da nasa hukuncin, ga su a takaice:

1. Idan mai Mahaifar Matarsa ce:

Idan mace mai mahaifar mata ce ta mai maniyyin, to a nan dan nasa, saboda maniyyinsa ne da kuma kwayoyin halittar da aka dauko daga maniyyin matarsa, aka kuma sanya a mahaifar kishiyar matarsa, kuma ita wannan matar tana karkashin inuwar aurensa; hukuncin Shari’ar Musulunci a nan shi ne, da na mai mallakan shmfida ne, kaman yanda Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya fadi cewa: ((Da na mai mallakan shimfida ne…)) [al-Bukhari da Muslim]

2. Idan mai Mahaifar ba Matarsa ba ce:

A nan kuma akwai surori biyu, ta yiwu tana da aure da wani mutum na daban, ta kuma yiwu ba ta da aure, ga bayanin kowane daya daga ciki a takaice:

a) Idan tana da Aure:

A nan za a danganta dan da mijinta ne, ba za a waiwayi mai maniyyi ba, saboda Hadisin da Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yake cewa: ((Da na mai mallakan shimfida ne, shi kuwa kwarto ba shi da komai sai dutse..)) [al-Bukhari da Muslim], ita Shari’ar Musulunci tana gina hukunce-hukuncenta ne a zahiri…

Wasu malamai sun tafi akan cewa dan da aka Haifa na mai maniyyin da aka cakuda da kwayoyin halittar ne, ba na mijin mai mahaifa ba, sun kafa hujja da cewa halal ne a cakuda maniyyin miji da kwayoyin halittar da aka ciro daga maniyyin matarsa, kawai abin da ya haramta shi ne shigar da shi cikin mahaifar wata matar ta daban, wannan haramcin kuwa ba zai yi tasiri wajen amshe masa ubancinsa, domin haramcin ya bijiro ne bayan haduwar maniyyin mijin da kwayoyin halittar matarsa, da haka jariri ya hadu kenan, babu abin da yake bukata daga mai mahaifa da ya wuce abincin da zai girma ya kuma sami habaka da bunkasa, za a iya cewa hukuncinsa a nan ya yi kama da yaron da iyayensa suka ciyar da shi da abincin haram, tabbas suna da laifi, amma wannan laifin ba zai hana a danganta dan da su ba..

Abin da masu wannan fahimtar ba su lura ba a nan shi ne: shi fa babu wata dangantaka tsakanin mai maniyyin da mai mahaifar da za ta sanya a tabbatar masa da matsayin uba, dangantaka ko dalilan da suke sanya a tabbatar wa namiji da matsayin uba a shari’ar Musulunci uku ne: aure –sahihi ko batacce-, ko a sami shubuha wajen kusantar juna tsakanin namiji da mace, ko kuma macen ta zamo baiwarsa ce.

b) Idan ba ta da Aure:

A nan kuwa dan da aka haifar zai zamo da ne na mai maniyyin da aka cakuda kwayoyin halittar matarsa, dukan hakkokin da suke tsakanin da da uba sun hau kansa, haka ma haramcin aure sakamakon kusanci. A nan an kafa hujja da cewa: Wasu malamai sun tafi akan ingancin danganta dan zina zuwa ga mazinacin da ya sadu da ita idan mazinaciyar ba ta da aure, inda suka nuna cewa nan ne ma ya fi cancanta da wannan hukunci, domin asalin maniyyin miji da matar ba su fuskantar haramci a lokacin fito da su, da lokacin cakuda su.

Game da amsar wace ce uwarsa ta Shari’a tsakanin mai kwayoyin halitta da mai mahaifa kuwa, a tara a gaba, insha Allah..

Was Salamu alaikum.



© TASKAR SUNNA

No comments:

Post a Comment