Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Sunday, January 14, 2018

TSARIN DA MUSULUNCI YA SHIMFIDA WAJEN MU’AMALA DA WADANDA BA MUSULMI BA (5)



Dr Saleh Kaura :


A bayanin da ya gabata mun nuna irin yanda Alkur’ani Mai girma ya wajabta wa Musulmai girmama Annabawan Allah baki daya, musamman Annabawan Ahlul kitabi, wadanda Musulmai suke zaune tare da jama’ansu a gari ko kasa daya.. mun kuma yi alkawarin cigaba da kawo bayanin Alkur’ani Mai girma game da Ahlul kitabi, ga shi za mu cika wannan alkawari da muka yi…

ZANCE ALKUR’ANI GAME DA AHLUL KITABI (3)

Alkur’ani Mai girma ya yi maganganu mabambanta akan matsalolin da Ahlul kitabi suka shiga a karkashin mulkin danniya da zalunci a cikin tarihin rayuwarsu, ya kuma yabe su akan hakurin da suka yi wajen fuskantar ‘yan kama-karya da azzalumai, ya kuma yaba masu game da tsayawansu akan akidarsu ba tare da sun kauce ba, duk kuwa da tsangwama gami da zaluncin da suka fuskanta.

Alal misali: Fir’auna ya tsangwami Yahudawa, ya azabtar da su da nau’o’i iri-iri na azaba, abin da ya kai shi ga farautarsu domin ya halaka duk wani da namiji da aka haifa wa Bayahude, sa’ilin da kuna yake barin ‘ya mace da aka haifa, ita ma domin biyan bukatunsa da na ‘yan amshin shatansa, duka wannan labari ne da Alkur’ani mai girma ya kawo, yana mai nuna rashin amincewa da wannan bakin zalunci da aka yi shi a karkashin mulkin danniya da kama-karya.. Sannan kuma Allah ya bayyana manufar karya gwamnatin Fir’auna da ya yi, ya yi haka ne domin Yahudawa da suka sha wahala su ji dadi, su kuma sami natsuwa, na dauka masu fansa daga wannan dan kama-karya da ya tsangwame su a tsawon lokaci, Allah Mai girma yana cewa: ((Kuma muna son mu yi wa wadanda aka murkushe wata baiwa ce, mu mayar da su su zamo shugabanni, mu kuma sanya su gaje abubuwan da wadancan suka bari.. mu damka masu iko a bayan kasa, mu nuna wa Fir’auna da Hãmãna da rundunoninsu abubuwan da suke tsoro..)) [al-Kasasi: 5-6].

Haka ma Alkur’ani Mai girma ya yi magana akan matsin da Kiristoci suka fuskanta a hannun wasu ‘yan mulkin kama-karya din da tarihi ya yi masu suna da “As’habul uhdud”, mutanen da suka haka rami, suka kuma cika shi da guma-gumai, suka kunna wuta, suna jefa Kiristocin da suka yi imani da Allah Madaukakin Sarki a ciki, Allah yana cewa: ((Lallai Allah ya tsine wa wadanda suka haka rami mai zurfi a kasa.. Wadanda suka kunna wuta da guma-gumai da suka hurata domin azabtar da muminai.. A lokacin da suke zazzaune a gefen ramin suna ganin yadda muminai suke azabtuwa… Suna cikin hankalinsu lokacin da suke aikata abin da suke aikatawa na azabtar da muminai.. Ba wani abu ne laifin muminai ba, sai imaninsu da Allah mai cikakken karfi da ake tsoron azabarsa, mai kuma yawan godiyar da ake kwadayin ladansa)) [al-Buruj: 4-8]. Saboda wannan tsangwama da azabarwa da Kiristoci suka fuskanta ne Allah ya la’anci wadancan azzaluman, ya kuma nesanta su daga rahama, nesantawa ta har abada.

Alkur’ani mai girma ya yi wa Kiristocin Roma albishir da nasara akan Parisawa masu bautan wuta, a cikin wasu ‘yan shekaru kadan masu zuwa, ya kuma sanya ranar da wannan nasara za ta zo, ta zama ranar farin-ciki ga muminai, domin Allah ne ya ba su nasarar, Allah mai girma yana cewa: ((Alif, Lam, mim.. lallai an ci nasara akan Romawa a can kusa da garin Larabawa, amma su ma za su yi nasara bayan wannan nasarar da aka yi akansu, a cikin wadansu shekaru ‘yan kadan, duk abubuwan da suke a kafin a sami nasara akansu, da bayan sun yi nasara, duka na Allah ne, lallai a wannan ranar muminai za su yi farin-ciki da nasarar da Allah ya ba su..)) [ar-Rum: 1-5].

Lallai wannan yana nuna irin goyon bayan da addinin Musulunci yake yi wa Kiristoci na samun nasara akan Parisawa masu bautan wuta, da haka za mu gane cewa addinin Musulunci bai kalli Kiristoci a matsayin hatsari ne a cigabansa, da har za su iya hana shi cigaba da yaduwa ba, bal ma ya fifita su akan wasunsu da suke bauta wa wani abu na daban koma bayan Allah, wannan yana nuna irin yanda Alkur’ani mai girma ya tabbatar da kusanci tsakanin Musulmi da Kiristoci akan kusanci da wadancan da ba su da dangantaka da wahayi, domin akwai wurare masu yawa da masu addini za su iya yin taimakekeniya a tsakaninsu.

A bayani mai zuwa –insha Allah- za mu tabo wasu ayoyi da suka yi magana akan daukacin wadanda ba Musulmai ba, suna masu bayyana yanda ya wajaba a zauna da su..

Saleh Kaura

© TASKAR SUNNA

No comments:

Post a Comment