Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Tuesday, January 9, 2018

Gobara ta kashe mutane 5 a wani gidan sayar da abinci a Indiya

Mutane 5 ne suka mutu sakamakon wata gobara da ta kama a gidan sayar da abin a Kasar Indiya.

Sanarwar da Rundunar 'Yan sandan Indiya ta fitar ta ce, gobarar ta kaa gidan abincin a yankin Bangalore da ke Kudancin Kasar.

An sanar da cewa, gobarar ta kama da sanyin safiya kuma ba a san musabbabinta ba.

Sanarwar ta kuma ce, an aike da jami'an kashe gobara zuwa yankin, bayan kashe wutar sai aka ga jikkunan mutane 5 da ke aiki a gidan sayar da abincin wadanda suke kwana a saman benen wajen.

An fara gudanar da binciken gano musabbabin kamawar gobarar.

A watan da ya gabata ma gobara a garin Mumbai na Indiya ta kama wani gidan sayar da abinci inda mutane 15 suka mtu.

No comments:

Post a Comment