Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Wednesday, January 10, 2018

Amurka na shirin yakar Koriya ta Arewa da karfin soja



Wata mujalar Amurka mai suna Wall Street Journal ta rawaito cewar gwamnatin shugaba Donald Trump na shirin kaiwa Koriya ta Arewa harin soja.
Mujalar ta kara da cewa, a dai-dai lokacin da Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu ke kokarin sulhunta tsakaninsu ta hanyar warware matsalolin su ta hanyar lumana ne shugaba Trump ke anniyar takalar tsuliyar dodo.
Haka kuma an bayyana cewar hukumomin Amurka na nazari akan yuwuwar kaiwa Koriya ta Arewa harin soja ba tare da haifar da babbar yaki, da ka iya kunsar kasashen yankin ba.
Bayan zaman sulhun da Koriyar biyu su ka gudanar, wani jami'in Koriya ta Arewa ya shaidawa kafar yada labaran Reuter da cewa makaman nukiliyar Koriya ta Arewa an kera su ne don kalubalantar Amurka kachal.

No comments:

Post a Comment