Dr. Saleh Kaura :
Ya 'yan uwana ku zo mu dan dakata kadan a gaban wannan zargi mai raushi da Ubangiji Mai girma yake yi wa dan Adam .. a kullum na karanta Alkur'ani Mai girma, da zaran na zo wurin wannan ayar, sai na maimaita sau biyu, ko uku, ko hudu, ina kuma cike da jin radadi gami da kunyar Allah Mai girma da buwaya, Allah yana cewa: ((Loakacin da muka ce wa Mala'iku: ku yi wa Annabi Adam sujada, sai suka yi sujadar, banda Iblis da ya kasance a cikin aljannu, shi ne ya qi bin umurnin Ubangijinsa... yanzu shi da zuri'arsa za ku dauka a matsayin majibinta al'amurranku koma baya na, bayan kasancewar shi makiyinku ne? ai kuwa tir da wannan sauyi na azzalumai))...
Shin kuna lura da wannan zargin kuwa?!
Allah Mai girma da daukaka fa cewa yake yi : Na kori Iblis ga barin hanyarku a lokacin da na karrama ku.. Na la'ance shi saboda ku.. Yanzu kuma ga shi kuna kawar da kai ga bari na.. Ni ne kuma Ubangijinku Mai yawan rahama da karamci a gareku.. Amma kuma sai kuka dauki wannan makiyin naku da na kore shi saboda ku a matsayin majibincin al'amarinku koma bayana!!
Allah da yake sonmu, wanda ya yi mana -bal yake mana - komai shi ne za mu juya wa baya, mu kama makiyin mu wanda ba ya son mu da komai na alhairi!!..
Wannan wane irin zaluntar kai mai matukar muni ne haka?!!..
(C) TASKAR SUNNA

No comments:
Post a Comment