Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya tausaya wa ‘yan Najeriya kan tsananin wahalar mai da kasa ta fada a daidai ana bikin Kirismeti.
Osinbajo ya bayyana haka ne da yake zazzagayawa wasu gidajen mai a jihar Legas a jajibarin Kirismeti.
Da ya ke zantawa da mutanen dake layin mai ya nuna rashin Jin dadin sa ganin yadda mutane ke takure a waje daya saboda wahalar Mai.
Ya ce bayan zagaye da yake yi domin duba halin da aka Shiga, shugaban kamfanin Mai na kasa na Abuja yana kokarin sa don ganin man ya wadata.
An fada tsananin wahalar mai a kasar nan ne makonni biyu da suka wuce inda gwamnati take ta yin alkawarin cewa za a samu man kafin bikin Kirismeti amma hakan bai yiwu.
Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar zuwa safiyar litinin, maimakon a sami sauki abin sai kara gaba yayi.