Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Saturday, January 6, 2018

'Yan Book Haram 700 Sun mika wuya


Rundunar sojin Najeriya ta ce kimanin mayakan kungiyar Boko Haram 700 sun mika wuya bayan ta gama yin luguden wuta a sansanonin da suke boye.
Rundunar samar da tsaro ta Operation Lafiya dole ta ci gaba da kai hari kan mayakan Boko Haram a yankin tafkin Chadi inda aka raunata shugaban wani bangare na kungiyar Mamman Nur, sannan kuma an kashe daya daga cikin matansa a kai harin, in ji wata sanarwa da daraktan hulda da manema labarai na rundunar Kanal Onyema Nwachukwu ya fitar.
Har ila yau, kimanin 'yan kungiyar 250 ne daga sansanin Albarnawy suka mika wuya ga hukumomin Najeriya sakamakon ruwan wuta ta sama da rundunar Operation Lafiya Dole ta yi musu.
Yawancin masu tayar da kayar bayan da suka tsere wa harin yanzu sun yi amfani da damar hukumar kare hakkin bil'adama ta "AMNESTY", wadda gwamnatin Najeriya ta bayar da dama ta mika wuya ga rundunar sojin Najeriya.
Daga cikin mayakan da suka tsere sun hada da manya da kananan kwamandodin bangaren Albarnawy, wadanda yanzu suka yi yunkurin sajewa a cikin jama'a, a kewayen Kano, da Geidam, da kuma Gashua. Daya daga cikinsu shi ne Bana Bafui.
Dadin-dadawa, kusan mayakan 700 ne suka mika wuya ga sojojin a yankin Monguno, bayan da dakarun sojin suka gama bude musu wuta.
Tuntuni gwamnatin Najeriya ta bayar da damar yin hakan, ta hanyar gabatar da shirin "Operation SAFE CORRIDOR", ga masu tayar da kayar bayan da suka mika wuya don kansu inda za a sauya musu mugun tunanin da yake zukatansu da kuma ba su ayyukan yi.
Yanzu haka kusan mayakan 300 da suka mika wuya suna cin gajiyar wannan shiri.
"Mun yi kira ga mayakan Boko Haram da su zub da makamai su y amfani damar shirin "Safe Corridor", ta hanyar mika wuya ga rundunar soji a kowanne yanki mafi kusa da su. Mun tabbatar musu da tsaron lafiyarsu da sauya musu mugun tunanin da yake zukatansu da kuma ba su ayyukan yi", in ji sanarwar.

BBC HAUSA

No comments:

Post a Comment