Fajirsa Blog

TATTAUNA ALAMURAN DASUKA SHAFI ADDINI, LABARAI, NISHADI, SADA ZUMUNTA

Sunday, January 7, 2018

Sabon rikici ya barke a Taraba


Al'amarin ya faru ne a wasu yankunan karamar hukumar Lau, da Katibu da kuma sauran kauyukan da ke kewaye da yankin.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa, "Wasu mutane ne da ake zargin Fulani ne suka kai harin da yin harbe-harbe da kuma cinna wa gidajen jama'a wuta".
"Yanzu haka muna da mutane 25 da aka kashe ban da wadanda suka gudu amma aka bi su a kan mashin aka harbe".
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar David Simal ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin.
Ya kuma kara da cewa, "An fara kai harin ne tun ranar Juma'a, kuma ko ranar Asabar ma mutum hudu ne suka rasu ranar Lahadi kuma mutane da dama ne suka mutu, amma kawo yanzu ba za mu iya tabbatar da adadinsu ba".
"An samu mutanen da suka jikkata kuma tuni aka garzaya da su asibi". In ji kakakin rundunar.
Zaman dar-dar na sake karuwa a yankunan na jihar Taraba, sakamakon rikice-rikice da hare-hare da ake samu musamman a kwanakin baya-bayan nan.

No comments:

Post a Comment