GABATARWA:
Assalamu Alaikum.
Sufanci hanya ce da take kira zuwa ga
gyaran zuciya, da sada ta da Allah madaukakin Sarki, saboda zukatan su
zama masu cikakkiyar biyayya da mika wuya gare shi ta hanyar aikata abin
da yayi umarni da barin abinda yayi hani, Kamar dai yadda Al-Qur`ani da
Hadisi suka yi nuni da kalmomi maban-banta, kamar (Tazkiyah – Ihsan –
Akhlaq – Tarbiyah) wadanda suka zo a Qur’ani da Sunna suna dauke da
wannan sakon. Sahabbai (Allah ya Kara masu yarda) sun rayu karkashin
babban jagora wanda shine, Masani, Malami, Alkali, Mai tarbiya, shugaban
siyasa kuma jagoran yaki baki daya, hakan ne ya bada daman a sami
sahabbai wadanda suka yi fice a daya daga bangarorin, kamar wajen Ilimi
da Ilmantarwa, tarbiya, da shiryatarwa, Fatwa da alkanci, Siyasa da
jagoranci, kai har ma Yaki don kare ta’addanci. Anan ne aka sami
AHLUSSUFFAH wadanda suka yi kokarin nesanta kansu daga rudin rayuwar
Duniya tare da juyar da hankalin su zuwa yawaita ibada, zikirin Allah,
neman Ilimi da jiran JIHADI don daukaka Kalmar Allah, kuma wannan
matafiyar taci gaba da yaduwa daga nan har suka koyar da mabiyansu
(Tabi’ai) da na bayansu (Atba’ut Tabi`un), hakan yayi ta wanzuwa har
wasu tsarkakan bayi na wannan zamani suka sami rabon su a ciki.
Lokutan da fituntunu suka fara yaduwa
tsakanin musulmi, zukata suka fara karkata zuwaga rudin Duniya, dai-dai
lokacin da ake cikin matsanaciyar bukatar wadanda zasu sadaukar da
kawunansu ga Musulunci sai wadannan magadan sahabban suka fara kebance
mutane suna tarbiyan su kan hanyar sufanci domin daukan nauyin dake kan
musulmai na yada Musulunci da ilimi, Kamarsu Imam Hasan al-Basry.
Tsakanin wanan lokacin ne aka sami Kalmar SUFANCI, bayan ma’nansa da
manufansa da ayyukan sa na gyara zukata da sada ta da Allah sun tabbata
da diga-digan su.
Manyan jigon ayyukan Sufaye sune: –
Tsarkake zukata ta hanyan karatun Kur’ani da Azkar din dasu suka
inganta. – Kyautata fuskantar Allah ta hanayar biyayya ga umarnin sa da
barin hane-hanen sa, tare da kyautata zamanta-kewa da bayin sa. – Raya
soyayyar Annabi Muhammad sallal Lahu alaihi wasallam a zukata tare da
aiki da abin da yazo dashi. – Yada Ilimi da kokarin daukaka Kalmar Allah
a kowane hali mutum yake. – Samar da soyayyar juna tsakanin musulmi da
zaman lafiya tsakanin mabiya addinai maban-banta. – Kira zuwa ga Allah
ta hanyoyin da Musulunchi ya gindaya. A karkashin sufanci aka samar da
DARIKUN SUFAYE kamar yanda aka sami MAZHABOBI a ilimin Fiqhu dana Tauhid
da sauransu, duba zuwa ga sunnonin Manzon Allah sallal Lahu alaihi
wasallam wadanda suka zo suna kwadaitar da mutane zuwa ga ayyuka masu
kyau, sai malaman sufanci suka sha ban-ban wajen fifita wani aiki a kan
wani, ko wacce hanya tafi wata, ba tare da karyata dayan ba ko rage masa
matsayi. Wannan shafi zai kokarin samar da bayanai gamsassu akan wannan
makarantar, kama daga manufan SUFANCI da ayyukansa a aikace da kuma
takaitaccen gudummawar da sufanci, sufaye suka bayar a Musulunci.
Sheikh Dr. Ibrahim Ahmad Maqari
No comments:
Post a Comment